Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Da Falasdinawa Suna Tattaunawa Kan Tsaro - 2003-06-23


Shugabannin tsaron Isra'ila da Falasdinawa suna ganawa domin tattauna yadda za a mayar da batun kula da tsaro hannun Falasdinawa a wasu yankunansu da Isra'ila ta mamaye.

Janar Amos Gilad na rundunar sojojin Isra'ila da babban jami'in tsaron Falasdinawa, Mohammad Dahlan, sune suke jagorancin wannan tattaunawa da ake yi yau litinin a tashar binciken Erez dake bakin iyakar Isra'ila da zirin Gaza.

Batun da za a tattauna a kai shine janye sojojin Isra'ila daga Gaza, amma kuma sai idan Falasdinawa zasu tabbatar da tsaron Isra'ila.

Firayim ministan Falasdinawa, Mahmoud Abbas, yana kokarin shawo kan 'yan kishin Falasdinu da su dakatar da hare-haren da suke kaiwa kan 'yan Isra'ila, bisa fatar cewa wannan zai sanya Isra'ila ta janye sojojinta daga yankunan Falasdinawa.

Janar Gilad ya ce Isra'ila ba ta son a shirya tsagaita wuta na wucin gadi, tana so ne a kawo karshen hare-hare baki daya.

XS
SM
MD
LG