Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cire Hong Kong Daga Cikin Jerin Kasashe Masu Fama Da Cutar SARS - 2003-06-23


Hong Kong ta ce tana shirya matakan bunkasa yawon shakatawa da bude idanu, da yake a yanzu an cire ta daga cikin jerin kasashen da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta zana na masu fama da cutar SARS.

A yau litinin hukumar bunkasa yawon shakatawa ta Hong Kong ta bayar da sanarwar shirin wanda ya hada da rangwamen kudin jirgi da na otel, da na abinci da kuma na sayen kayayyaki a watannin Yuli, da Agusta da kuma Satumba.

Kamfanin safarar jiragen sama na Cathay Pacific mai hedkwata a tsibirin Hong Kong ya ce zai raba tikiti dubu 10 kyauta a zaman gudumawarsa ga yunkurin bunkasa yawon an shakatawa. haka kuma, kamfanin ya ce nan da watan Satumba yake shirin maido da dukkan zirga-zirgar da ya soke a sanadin barkewar annobar cutar ta SARS.

A yau litinin Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta cire Hong Kong daga jerin kasashe masu fama da cutar SARS, kwanaki 21 a bayan da aka samu harbuwar mutum na karshe da wannan cuta a tsibirin.

XS
SM
MD
LG