Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Liberiya Suna Ci Gaba Da Barin Wuta Kan Birnin Monrovia - 2003-06-25


'Yan tawayen Liberiya suna ci gaba da yin barin wuta kan unguwannin bayan garin Monrovia, babban birnin kasar, yayin da shugaba Charles Taylor ya ce shi da sojojinsa zasu yaki 'yan tawayen har sai sun ga abinda ya ture wa buzu nadi.

An ji kararrakin fashe-fashe jiya talata da daddare da kuma yau laraba da safe a Monrovia, matakin da ya rushe shirin tsagaita wutar da aka yi aiki da shi. Wasu rahotanni sun ce 'yan tawayen sun kusanci wata gada mai muhimmanci da ta tsallaka kogin Saint Paul, watau tazarar kilomita kadan kawai tsakaninsu da tsakiyar birnin na Monrovia.

Tuni fararen hula suka gudu daga unguwannin bayan garin Monrovia suka doshi tsakiyar birnin, inda suka nemi mafaka a sansanonin 'yan gudun hijira dake can.

'Yan tawayen sun doshi Monrovia a karon farko tun bayan da sojojin gwamnati suka maida su baya daga kusa da birnin a farkon watan nan. Sojojin gwamnati da na 'yan tawaye suna zargin juna da laifin sake barkewar fada.

A ranar litinin, kungiyar 'yan tawayen "L.U.R.D." ta yi barazanar kauracewa tattaunawar neman zaman lafiyar da ake yi a Ghana. Kungiyar ta zargi masu shiga tsakani da laifin kasa tabbatar da cewa shugaba Taylor ya cika alkawarin da ya dauka na yin murabus cikin wata guda a karkashin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma.

XS
SM
MD
LG