Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Liberiya Ta Ce Ta Fatattaki 'Yan Tawaye Daga Tsakiyar Birnin Monrovia - 2003-06-26


Ministan tsaron Liberiya ya ce sojojin gwamnati sun fatattaki 'yan tawaye daga tsakiyar birnin Monrovia, a bayan da aka gwabza mummunan dauki-ba-dadi.

Daniel Chea ya ce sojoji masu biyayya ga shugaba Charles Taylor sun kori 'yan tawaye daga yankin tashar jiragen ruwan birnin, ya kuma ce zasu ci gaba da korar 'yan tawayen zuwa bayan gari.

Wasu kungiyoyin 'yan tawaye biyu sun kama fiye da kashi 2 daga cikin 3 na yankunan kasar Liberiya, amma sai a ranar talatar nan suka shiga cikin Monrovia.

Gwamnati ta ce an kashe fararen hula da yawa a fada na baya-bayan nan. Wasu daruruwa sun ji rauni, yayin da 'yan gudun hijira ke kwarara zuwa cikin babban birnin.

A jiya laraba, jakadan Britaniya a Majalisar Dinkin Duniya, Jeremy Greenstock, ya bayar da shawarar cewa a tura rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka zuwa Liberiya.

Ya ce tsoma bakin kasashen waje, kamar yadda Faransa ta yi kwanakin baya a kasar Ivory Coast, zai taimaka, kuma abin marhabin ne.

Sai dai kuma babu wata alamar cewa Amurka tana da shirin yin hakan.

XS
SM
MD
LG