Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraqi Ta Yi Watsi Da Shirinta Na Kera Makaman Nukiliya Fiye da Shekaru 12 Da Suka Shige - 2003-06-26


Wani kakakin hukumar kula da makamashin nukiliya ta MDD, ya ce Iraqi ta yi watsi da shirinta na kera makaman nukiliya fiye da shekaru 12 da suka wuce.

Wannan kakakin hukumar kula da makamashin nukiliyar ta duniya, Mark Gwozdecky, ya fada yau alhamis a birnin Vienna, cewar wasu na'urorin nukiliyar da ake fadin cewa an gwano cikin 'yan kwanakin nan, kayayyaki ne da aka kai su can Iraqi tun kafin shekarar 1991, kuma wannan ya tabbatar da gaskiyar ikirarin da hukumar ta yi cewa Iraqi ba ta da wani shiri na kera makaman nukiliya.

Wannan furuci nasa ya zo kwana guda a bayan da hukumar leken asirin Amurka ta ce wani tsohon masanin kimiyya na Iraqi ya mika musu na'urorin wani injin gas.

Jami'an leken asirin Amurka suka ce wannan masanin kimiyya mai suna Mahdi Obeid ya binne injin ne shekaru 12 da suka shige a gidansa a bisa umurnin gwamnatin Saddam Hussein.

Kakakin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya ce wannan bayani yayi daidai da rahotannin da suka bayar can baya ga Kwamitin Sulhun MDD.

XS
SM
MD
LG