Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Da Kofi Annan Zasu Tattauna Batun Liberiya - 2003-07-14


Shugaba Bush zai gana da babban sakataren MDD, Kofi Annan, yau litinin a fadar White House domin tattaunawar da ake sa ran zata mayar da hankali kan batun kasar Liberiya mai fama da yaki.

Wannan ganawa ta su ta zo a bayan ziyarar da dukkan mutanen biyu suka kai nahiyar Afirka, kuma daidai lokacin da gwamnatin Liberiya da babbar kungiyar 'yan tawayen kasar suke zargin juna da laifin keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi wata guda da fara aiki da ita.

Gwamnatin ta Liberiya ta fada a yau litinin cewa 'yan tawayen sun doshi babban birnin kasar, Monrovia, a bayan da suka kai farmaki kan sojojin gwamnati a wajen birnin cikin 'yan kwanakin da suka wuce.

Shugabannin 'yan tawaye suka ce suna kare kansu ne daga hare-haren gwamnati.

Daga cikin batutuwan da Mr. Annan da Mr. Bush zasu tattauna har da yiwuwar tura sojojin kiyaye zaman lafiya na Amurka zuwa kasar ta Liberiya.

XS
SM
MD
LG