Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Kira Ga 'Yan Tawayen Burundi Da Su Tattauna... - 2003-07-14


Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kira ga 'yan tawayen Burundi da su dakatar da hare-haren da suke kaiwa, kwana guda a bayan da ta umurci dukkan ma'aikatan jakadancin da ayyukansu ba su da muhimmanci su bar wannan kasa dake yankin tsakiyar Afirka.

Har ila yau Amurka ta gargadi Amurkawa da su yi nesa da Burundi, ta kuma yi kira ga wadanda ke can da su yi kokarin fita.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje, Richard boucher, ya fada a yau litinin cewa Amurka tan sake nanata rokon da ta yi wa 'yan tawayen kabilar Hutu da su watsar da tayar da fitina su tattauna da gwamnatin Burundi.

An kashe mutane akalla 174 tun lokacin da 'yan tawayen suka kaddamar da kan Bujumbura, babban birnin kasar, a makon da ya shige.

Mataimakin shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, yana shirin ziyartar Burundi a wannan mako, a lokacin rangadin da zai yi zuwa kasashen dake yankin manyan tabkunan Afirka.

XS
SM
MD
LG