Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kasuwa Zai Shugabanci Gwamnatin Rikon Kwarya A Liberiya - 2003-08-22


'Yan tawaye da kuma jami'an gwamnatin Liberiya sun zabi wani dan kasuwa na birnin Monrovia domin ya shugabanci gwamnatin rikon kwaryar da zata jagoranci kasar bayan yaki.

A jiya alhamis aka nada Gyude Bryant a zaman shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Liberiya. Ana daukarsa a zaman mutumi mai neman hada kan jama'a wuri guda wajen yanke shawara, kuma dan babu-ruwanmu a fagen siyasa.

Mr. Bryant zai amshi ragamar mulki daga hannun shugaban kasar na yanzu Moses Blah a watan Oktoba. Zai jagoranci sabuwar gwamnati na tsawon shekaru biyu, tare da shirya zaben dimokuradiyya a shekara ta 2005.

Mr. Bryant ya shaidawa kafofin yada labarai na kasa da kasa jiya alhamis cewar daya daga cikin abubuwan da zai fara yi shine karbe makaman 'yan tawayen Liberiya. Ya kara da cewa ba ya son a kafa kotun bin kadin laifuffukan yaki a kasar Liberiya a saboda yayi imani da cewa illar yin haka ta fi amfaninsa yawa.

Kafa gwamnatin rikon kwarya a Liberiya na daya daga cikin muhimman tanade-tanade da dama na yarjejeniyar zaman lafiya mai dimbin tarihi da aka cimma ranar litinin da ta shige da nufin kawo karshen yakin basasar kusan shekaru 14 a kasar.

XS
SM
MD
LG