Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana ta Tura Sojojinta Domin Kara Karfin 'Yan Kiyaye Zaman Lafiya A Liberiya - 2003-08-23


Ghana zata tura sojojinta zuwa Liberiya domin karfafa rundunar kiyaye zaman lafiyar da Nijeriya take yi wa jagoranci wadda take kokarin tabbatar da yin aiki da yarjejeniyar da zata kawo karshen yakin basasar shekaru 14 a can.

Jiya Jumma'a aka shirya wani ayarin sojojin Ghana zai isa Monrovia. Tun kusan makonni biyun da suka shige sojojin kiyaye zaman lafiya su kimanin 900 daga Nijeriya suke Monrovia, babban birnin Liberiya.

Akwai wasu kasashen na Afirka, ciki har da Afirka ta Kudu, da Habasha (Ethiopia), da Mali da kuma Senegal, wadanda suka yi alkawarin ba da gudumawar sojoji ga wannan runduna.

Ana sa ran yawan sojojin da za su yi aiki a wannan runduna zai wuce dubu uku.

A halin da ake ciki, shugaban rikon kwarya na Liberiya, Moses Blah, yana rangadin kasashe makwabta domin tattauna halin da ake ciki a kasarsa. Tuni dai har ay ziyarci Ivory Coast (Cote d'Ivoire) da Guinea da kuma Nijeriya.

XS
SM
MD
LG