Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Ya Ce Ire-Iren Al-Qa'ida Suna Sulalewa Zuwa Iraqi. - 2003-08-23


Shugaba Bush ya ce Iraqi tana rikidewa zuwa fagen daga a ci gaba da yakin da ake yi da ta'addanci.

Mr. Bush ya ce 'yan ta'addar kasashen waje "ire-iren al-Qa'ida" suna shiga Iraqi domin takalar sojojin kawancen da Amurka take yi wa jagoranci a saboda, a cewarsa, "ba su kaunar ganin Iraqi ta zamo mai bin tafarkin dimokuradiyya."

A lokacin da yake magana a Seattle ta jihar Washington jiya jumma'a, Mr. Bush ya bayyana Iraqi a zaman babbar daga a yakin farko na karni na 21. Ya ce Amurka tana bukata, kuma zata yi marhabin da, karin sojoji daga kasashe kawaye domin su yi gadin wuraren da watakila 'yan ta'adda zasu kaiwa hari a Iraqi.

Shugaba Bush ya ce yin haka zai bai wa sojojin Amurka sukunin komawa ga farautar 'yan ta'adda da mutanen da ya kira 'yan daba daga hambararriyar gwamnatin Saddam Hussein.

Shi kuma mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka, Richard Armitage, cewa yake yi hukumomi a Washington sun damu matuka da yadda 'yan ta'adda ke kwarara cikin Iraqi daga Sa'udiyya da Iran da kuma Syria.

Mr. Armitage ya fadawa gidan telebijin na al-Jazeera a wata hirar ads uka yi cewar ba wai Amurka tana zargin gwamnatocin wadannan kasashe da alhakin wannan abu ba ne. Amma kuma ya ce ba a tsayar da wadannan 'yan ta'adda a bakin iyaka.

XS
SM
MD
LG