Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Yi Barazanar Yin Watsi Da Yarjejeniyar Dakile Yaduwar Makaman Nukiliya - 2003-09-14


Iran ta yi gargadin cewa za ta bi sahun Koriya ta Arewa, ta janye daga yarjejeniyar kasa da kasa wadda ta haramta yada makaman nukiliya.

Wakilin Iran a Hukumar Kula da makamashin nukiliya ta MDD, Ali Akbar Salehi, shi yayi wannan barazana a cikin wata hirar da yayi da wata mujallar kasar Jamus mai suna "Der Spiegel."

Mr. Salehi ya ce idan har ba za a iya warware tankiyar da ake yi tsakanin kasarsa da hukumar ba, to Iran zata tsame hannunta daga Yarjejeniyar Dakile Yaduwar Makaman Nukiliya.

A ranar Jumma'a hukumar ta MDD ta zartas da wani kudurin da ya bai wa Iran wa'adin nan da ranar 31 ga watan Oktoba da ta tabbatarwa da ita hukumar cewa ba ta da wani shiri na asiri na kera makaman nukiliya.

Rasha tana taimakawa Iran wajen gina injin sarrafa makamashin nukiliya, amma hukumomi a birnin moscow sun yi kira ga Iran da ta yi aiki da wannan kuduri na hukumar.

XS
SM
MD
LG