Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Zimbabwe Ta Ce Zata Daukaka Karar Hukumcin Da Wata Kotu Ta Yanke - 2003-09-20


Gwamnatin Zimbabwe ta ce zata daukaka karar hukumcin da wata kotu ta yanke inda ta umurci ita gwamnatin ta kyale wata jarida mai zaman kanta ta sake gudanar da ayyukanta.

A farkon wannan makon, 'yan sanda sun rufe ofisoshin jaridar mai suna "Daily News" suka kwace na'urorin kwamfuta da wasu kayayyakinta. Wannan matakin na gwamnati ya zo a bayan da kotun koli ta Zimbabwe ta yanke hukumcin cewar ayyukan da jaridar ke gudanarwa sun sabawa doka tun da ba ta yi rajista kamar yadda dokokin gwamnati suka bukata ba.

Masu wallafa jaridar sun rubuta takardar neman rajista. Har ila yau sun roki babbar kotun da ta hana 'yan sanda kai sumame a ofisoshin jaridar, a kuma kyale ta ta ci gaba da buga jaridu yayin da ake nazarin takardar neman rajistarta.

A ranar alhamis, wata babbar kotun Harare ta yarda da bukatar masu wallafa jaridar ta umurci gwamnati da ta kyale a ci gaba da buga jaridar ta "Daily News."

Amma kuma jami'an kamfanin jaridar sun ce 'yan sanda sun kasa yin aiki da umurnin kotun. Lauyoyi sun ce ana iya tuhumar 'yan sanda da laifin raina kurwar kotu idan sun ki yin aiki da wannan umurni.

XS
SM
MD
LG