Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isabel Ta Yi Barna Mai Yawa, Ta Kuma Kashe Mutane Akalla 17 - 2003-09-20


Sauran abinda ya rage na mahaukaciyar guguwar nan mai suna Isabwel, na ci gaba da katse wutar lantarki yayin da take ci gaba da ratsa yankin Ontario a kasar Canada dauke da iska mai tsanani da ruwan sama mai yawa.

Kafin nan kuwa, Isabel ta ratso ta nan yankin gabashin Amurka, inda ta katse wutar lantarkin gidaje da ofisoshi kusan miliyan 6, ta kuma kashe mutane akalla 17.

A yayin da aka fara maido da wutar lantarki a wasu wuraren jiya Jumma'a, jami'an kamfanonin wutar lantarki sun yi kashedin cewa za a dauki kwanaki, watakila ma har mako guda, kafin a maido da wutar lantarki a ko ina.

Ruwan da aka juye kamar da bakin kwarya ya sa koguna sun tumbatsa suka yi ambaliya, inda tituna a birane kamar Baltimore dake Jihar Maryland da Alexandria a Jihar Virginia, suka zamo tamkar koguna. An katse ruwan famfo a wasu sassan jihohin Carolina ta Arewa da Virginia.

A nan cikin birnin Washington da kuma yankunan dake kewaye, an rufe ofisoshin gwamnatin tarayya da na kananan hukumomi a rana ta biyu a jere jiya Jumma'a.

An bude filayen jiragen saman dake wannan yanki ga jiragen dake sauka, amma kuma jirage ba su fara tashi ba a saboda an tashi da su zuwa wasu birane can nesa kafin isowar wannan mahaukaciyar guguwa. Wannan mahaukaciyar guguwa ta sa an soke tashin jirage kusan dubu shida a filayen jirage guda 20.

Jiya Jumma'a da maraice, shugaba Bush ya ayyana wasu bangarorin jihar Maryland a zaman wadanda bala'i ya abka wa. Tuni da ma an bayar da agajin gaggawa na gwamnatin tarayya ga jihohin Carolina ta Arewa da Virginia domin tallafawa ayyukan gyare-gyare.

XS
SM
MD
LG