Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Madugun 'Yan Tawayen Burundi Ya Ce An Cimma Daidaituwa Kan Wani Muhimmin Batu - 2003-10-07


Babban madugun 'yan tawayen kasar Burundi ya ce ya cimma daidaituwa da gwamnati a kan wasu muhimman batutuwa na tsaro, amma kuma bai ce ana dab da cimma kammalalliyar yarjejeniya ta zaman lafiya ba.

Madugun kungiyar 'yan tawayen dake kiran kanta Dakarun Kare tafarkin Dimokuradiyya, Pierre Nkurunziza, ya ce bangarorin biyu sun daidaita a kan yadda za a yi da 'yan tawayen kabilar Hutu a cikin rundunar sojojin kasar da 'yan kabilar Tutsi suka kanainaye da kuma a cikin rundunar 'yan sanda.

Bai bayyana ko gwamnati ta amince da bukatar da ya gabatar tun farko cewar a bai wa dakarunsa kashi 40 daga cikin 100 na mukamai a rundunonin ba.

Aikin dake gaban sassan biyu a yanzu shine na yadda za a raba mukamai a gwamnatin rikon kwarya da kuma majalisar dokoki ta kasa da za a kafa.

Madugun 'yan tawayen yana tattaunawa da shugaba Domitien Ndayizeye na Burundi a kasar Afirka ta Kudu. Wannan ita ce tattaunawar farko ta raba iko da sassan ke gudanarwa tun bayan watsewar taron kolin da suka yi cikin watan Satumba ba tare da cimma komai ba.

XS
SM
MD
LG