Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Tana Shirye-Shiryen Yin Abin Tarihi: Cilla Dan Adam Zuwa Samaniya - 2003-10-14


'Yan sama jannati uku na kasar China dake kokarin zamowa na farko da kasar zata tura cikin sararin samaniya sun isa dandalin harba kumbon kasar dake hamadar Gobi a yankin arewa maso yammacin China.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua na China ya ce a yau talata ne za a zabi dan sama jannati na farko daga cikin wadannan uku, kuma a gobe laraba za a cilla shi zuwa samaniya.

Wannan kumbo na China mai suna "Shenzhou-Five" ko kuma Kumbo Mai Tsarki a harshen Mandarin, zai tashi daga dandalin harba kumbo na Jiuquan gobe laraba da safe.

Ana sa ran kumbon ai zagaya duniya sau 14 a cikin sa'o'i 21 da zai yi yana shawagi kafin ya komo doron duniya.

Idan har China ta samu nasarar haka, zata shiga cikin sahun kasashe 'yan kalilan da suke iya cilla dan Adam zuwa sararin samaniya. A yanu dai, Amurka da Rasha ne kawai suke iya yin hakan.

XS
SM
MD
LG