Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Bayyana Taka Tsantsan Wajen Mayar Da Martani Ga Sabon Kudurin Da Amurka Ta Gabatar Kan Batun Iraqi - 2003-10-15


Ana yin taka tsantsan wajen mayar da martani ga sabon kudurin da Amurka ta yi wa gyaran fuska ta gabatarwa da Kwamitin Sulhun MDD a kan kasar Iraqi.

Babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya ce wannan sabon kudurin da Britaniya da Spain suka bi sahun Amurka wajen gabatarwa ba ya da wani bambancin kirki da wadanda aka gabatar a baya, koda yake ya takali wasu daga cikin batutuwan da ya koka a kai.

Rahotanni sun ambaci mukaddashin ministan harkokin wajen Rasha, Yuri Fedotov, yana fadin cewa Rasha tana shirin gabatar da sauye-sauye da dama ga wannan daftarin kuduri na Amurka.

Amurka tana son a jefa kuri'a kan wannan kuduri a cikin makon nan. Kudurin zai ajiye wa'adin ranar 15 ga watan Disamba ga Majalisar Mulkin Iraqi da ta gabatar da tsarin lokutan rubuta sabon tsarin mulki tare da gudanar da zabubbuka a kasar.

Amma wasu 'yan majalisar mulkin ta Iraqi sun ce zai yi wuya su iya gabatar da wadannan ayyuka cikin wannan lokaci.

XS
SM
MD
LG