Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Yi Gwajin Makami Na Uku Mai Linzami Dake Iya Daukar Kundun Nukiliya - 2003-10-15


Amurka ta yi kira ga kasashen yankin kudancin Asiya da su kai zuciya nesa, a bayan da Pakistan ta bayar da sanarwar gudanar da gwaji na uku na makami mai linzami da zai iya daukar kundun nukiliya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Richard Boucher, ya kuma yi kira ga Pakistan da abokiyar gabarta mai makaman nukiliya Indiya, da su fara tattaunawa na karfafa amana domin rage yiwuwar gwabzawa da makaman nukiliya a tsakaninsu.

Wannan furuci na jiya talata, ya zo sa'o'i kadan a bayan da rundunar sojan Pakistan ta ce ta kammala wasu gwaje-gwaje guda uku na wani makami mai linzami dake cikin matsakaicin zango da ake kira "Shaheen-One."

Wannan makami mai linzami yana iya cin zangon kilomita 700, tazarar da zata iya ba shi damar kai farmaki kan cibiyoyin da aka auna a tsakiyar kasar Indiya.

Indiya ta ce Pakistan ta ba ta sanarwar cewa zata gudanar da wannan gwaji tun kafin ta yi.

XS
SM
MD
LG