Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Harkokin Wajen Wasu Kasashe Uku Na Turai Zasu Yi Tattaki Zuwa Iran Kan Batun Nukiliya - 2003-10-21


Ministocin harkokin wajen kasashen Britaniya da Faransa da kuma Jamus za su gana da jami'an Iran a birnin Teheran yau talata a wani yunkuri na warware rikicin da ake yi kan shirin nukiliya na kasar.

Sakataren harkokin wajen Britaniya, Jack straw, ya shaidawa masu neman labarai a kan hanyarsa ta zuwa Teheran, cewa Iran tana da alhaki mai nauyi na tabbatarwa da al'ummar duniya cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne.

Ya ce shi da takwarorinsa, watau ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer da ministan harkokin wajen Faransa Dominique de Villepin, za su lallashi Iran da ta bayar da cikakken hadin kai ga Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya.

Hukumar ta bai wa Iran wa'adin nan da ranar 31 ga watan nan na Oktoba da ta tabbatarwa da duniya cewar ba ta fakewa da shirinta na samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya domin kera makamai.

XS
SM
MD
LG