Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takardun Masu Sauraron Sashen Hausa Na Muryar Amurka - 2003-10-21


Musa Dayyabu, mai adireshin Email kamar haka: daiyibu@yahoo.com, ya rubuto mana takarda ta duniyar gizo yana fadin cewa:

"Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuh. Ina mai farin cikin samun damar aiko maku da wannan sako nawa don in nuna murnata da farin ciki na da irin aiyukan da kuke gabatarwa a wannan sashi na Hausa, wanda yake matukar daukaka darajar Hausa. Allah ya kara taimaka mana, Amin. Bayan haka, ina son in rokeku wasu abubuwa...: Na farko shine ni mutum ne mai son bincike-bincike musamman na kimiyya, a kimiyyar ma abinda ya shafi Astronomy. Wannan yasa nake son in tambayeku ko zaku taimaka min da Web Sites da zan rika samun ire-iren wadannan sakonni, kuma ko zai yiwu in sami wani Web Site da suke offering On-Line Courses a wannan fanni.

Na biyu shine ina son ku tayani nema min adireshin E-Mail na kungiyoyin da ke gudanar da aiyukan Addinin Musulunchi a turai da amurka, da kuma hanyar da zan iya saduwa da su don amfanuwa da irin aiyukan da sukeyi, da kuma bada irin gudunmuwar da zan iya.

Na uku kuma shine ina rokon ku aiko min da hotunan ma'aikatanku ta adireshin E-Mail dina, wato daiyibu@yahoo.com...."

AMSA: Malam Dayyabu mun gode da wannan takarda ta ka. Babu shakka idan har kana sha'awar nazarin abubuwan da suka shafi samaniya da taurari da makamantansu, to kana da abokai da yawa a nan Sashen Hausa. Dandalin da ya kamata ka fara ziyarta idan kai mai sha'awar wannan fanni na ilmi ne, shi ne (www.astronomy.com) inda za ka samu labarai da kasidu masu yawa kan binciken sararin samaniya. Wani dandalin mai tarin bayanai da yawa kuma shi ne na Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, ko NASA, wanda ke dauke da kowane irin bayani kake nema, har ma da inda za ka samu kara ilmi kan wannan fanni da ma inda zaka samu gudumawar kudin karanta wannan fanni. Adireshin dandalin shine: (www.nasa.gov)

Game da kungiyoyin addinin Musulunci dake wannan bangaren duniya kuwa, babban dandalin da za ka iya ziyarta domin cikakken bayani shi ne na Kungiyar Musulmin Nahiyar Amurka ta Arewa, ko Islamic Circle of North America a turance. Adireshin dandalin shine: (www.icna.org) A nan za ka samu karin bayani na sauran kungiyoyi da makarantun Musulmi da masallatai. Mun gode kwarai.

XS
SM
MD
LG