Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Yarda Da Sabbin Matakai Masu Tsauri Na Binciken Masana'antun Nukiliyarta - 2003-10-22


Iran ta yarda sufetocin nukiliya na kasa da kasa su ringa gudanar da binciken ba-zata a masana'antun nukiliyarta, zata kuma dakatar da aikin tace makamashin karfen Uranium.

An bayar da sanarwar cimma wannan yarjejeniya kwanaki goma kafin cikar wa'adin da Hukumar Makamashin nukiliya ta Duniya ta bai wa Iran na ta tabbatarwa da duniya cewar ba ta kera makaman nukiliya.

An kuma cimma yarjejeniyar a bayan ganawar da aka yi a tsakanin jami'an Iran da ministocin harkokin wajen kasashen Britaniya da Faransa da kuma Jamus.

Wani jami'in Iran ya ce dakatar da tace karfen na Uranium na wani dan lokaci ne domin a samu damar gina yanayi na yarda da juna.

Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta duniya ta ce duk da wannan, tilas Iran ta bayar da cikakken bayani na shirye-shirye da ayyukanta na nukiliya na baya, tare da sanarwa a rubuce cewar zata sanya hannu kan takardar yarda da gudanar da binciken ba-zata a masana'antun nata.

XS
SM
MD
LG