Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton Ya Cimma Yarjejeniya Da Kamfanonin Sarrafa Magunguna... - 2003-10-24


Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton ya bayar da sanarwar cimma yarjejeniya da wasu kamfanonin harhada magunguna guda hudu domin sarrafawa tare da samar da magunguna masu rahusa na yaki da ciwon kanjamau ga kasashe masu tasowa.

A lokacin da yake magana jiya alhamis a birnin New York, Mr. Clinton ya ce a karkashin wannan yarjejeniya kudin wannan gaurayen magunguna uku da ake sha a kowace rana, zai komo kwabo 38 kawai a kudin Amurka, ko kuma kimanin naira 40, watau kusan kashi 1 cikin 3 kawai na ainihin kudin maganin.

Mr. Clinton ya bayyana yarjejeniyar a zaman gagarumin ci gaban dazai taimakawa masu fama da wannan cuta a wuraren da kusan babu wannan magani, saboda haka babu fata ta gari.

Wasu kamfanonin harhada magunguna uku na kasar Indiya da wani guda na kasar Afirka ta Kudu zasu samar da kofen wadannan magunguna uku da ake sha lokaci guda a kowace rana.

An cimma wannan yarjejeniya ce da Gidauniyar Clinton wadda ke aiki da kasashen Afirka da na Carribean da dama domin samar da kudaden yaki da cutar.

Shirin yaki da cutar kanjamau ta MDD da kungiyar agajin likitoci ta "Doctors Without Borders" sun yaba da cimma yarjejeniyar. Suka ce a yanzu, akwai alamun za a iya cimma burin Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya na samar da magunguna ga karin mutane miliyan uku masu fama da cutar nan da shekara ta 2005.

XS
SM
MD
LG