Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Shugaba George W. Bush Na Amurka Ga Musulmi Kan Azumin Watan Ramadan - 2003-10-28


Ina aikewa da gaisuwa ga Musulmi a nan Amurka da kuma a fadin duniya saboda shiga cikin wannan wata mai tsarki na Ramadan.

Ramadan shi ne wata mafi tsarki a addinin Musulunci, domin a wannan watan ne aka fara wahayin al-Qur'ani ga (Annabi) Muhammad (s.a.w.). Wannan wata na ibada da tsarkake zuciya, yana bai wa Musulmi damar mayar da hankali kan addininsu da kuma aikata umurnin Ubangiji. Ta hanyar azumi, da Salla, da zikiri da kuma yin sadaka, Musulmi a fadin duniya su kan sake sadaukar da kansu domin gudanar da rayuwa ta gaskiya, da yin da'a da kuma nuna tausayawa.

A duk tsawon tarihinmu, mabiya addinai dabam-dabam sun tsoma hannu wajen tsara dabi'un kasarmu. Addinin Musulunci, addini ne na zaman lafiya, kuma Musulmi sun bayar da gagarumar gudumawa ga kasarmu da kuma duniya baki daya. A matsayinmu na Amurkawa, muna mutunta 'yancinmu na yin addinin da muka yi imani da shi, kuma muna marhabin da mutane masu bin kowane irin addini. Ta hanyar yin aiki tare domin daukaka martabar 'yanci da fahimtar juna, muna kirkiro da makoma mai kyau ta fata ta gari da dama a nan gaba.

Mai daki na Laura tare da ni kai na muna mika muku sakon fatar alheri. Ramadan Mubarak.

XS
SM
MD
LG