Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahathir Mohammad Zai Yi Ritaya Yau Jumma'a - 2003-10-31


Shugaban gwamnatin da ya fi kowa jimawa kan mulki a yankin kudu maso gabashin Asiya, firayim minista Mahathir Mohammad na kasar Malaysia, zai yi murabus a yau jumma'a, a bayan ya shafe shekaru 22 kan wannan kujera.

A bayan ya sauka, sarki Syed Sirajuddin Putra Jamalullai na Malaysia, zai nada mukaddashin malam Mahathir, Abdullah Ahmad Badawi, a zaman sabon firayim minista.

A jawabin da yayi ga majalisar dokokin kasar jiya alhamis, firayim ministan mai barin gado, kuma dan shekaru 78 da haihuwa, ya ce yana da kwarin guiwa game da makomar kasar Malaysia. Har ila yau yayi watsi da sukar cewa wai gwamnatinsa tana keta hakkin jama'a.

Malam Mahathir, wanda bakinsa ba ya barin ya huce, zai yi ritaya a daidai lokacin da yake shan suka game da furucin da yayi cewar yahudawa ne suka fake da wasu suke gudanar da harkokin wannan duniya a yanzu.

Malam Mahathir ya ce ba a fahimci wannan kalami nasa ba ne, amma kuma ya ce ba zai nemi gafara ba. Ya ma shaidawa 'yan jarida jiya alhamis cewar zai ci gaba da fadin abinda ke cikin zuciyarsa ko da ya sauka daga kan wannan mukami.

XS
SM
MD
LG