Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rumsfeld Ya Ce Ana Samun Ci Gaba A Iraqi, Duk Da hare-haren Da Ake Kaiwa - 2003-10-31


Sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, ya ce ana samun ci gaba a kasar Iraqi, duk da munanan hare-haren ta'addanci da bama-bamai a fadin kasar cikin 'yan kwanakin nan.

Mr. Rumsfeld ya ce babu wata dabarar gajeren lokaci ta magance wadannan hare-hare a Iraqi.

Sakataren tsaron na Amurka yayi magana jiya alhamis, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da sanarwar janye ma'aikatanta 'yan kasashen waje daga Iraqi na wani dan lokaci a saboda fargabar tsaro.

Jami'an Amurka sun bayyana fahimtar matakan na MDD da kuma na Kungiyar Agaji ta Red Cross, wadda tun farko ta bayar da sanarwar janye wasu daga cikin ma'aikatanta ita ma.

A halin da ake ciki, 'yan sandan Iraqi sun ce an kashe mutum akalla daya, wasu da dama suka ji rauni a lokacin da wani abu yayi bindiga a tsakiyar birnin Bagadaza.

XS
SM
MD
LG