Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bayyana Damuwa Kan Rikicin Siyasar Kasar Sri Lanka - 2003-11-05


Amurka ta ce ta damu cewar rikicin siyasar dake kara yin muni a kasar Sri Lanka zai iya raunana shirin samar da zaman lafiyar da ake neman kullawa da 'yan tawayen Tamil Tigers.

A jiya talata, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta roki shugaba Chandrika Kumaratunga da firayim minista Ranil Wickremesinghe da su kulla sulhun siyasa domin su samu damar kawo karshen yakin basasar shekaru 20 a kasar.

A jiya talata, Ms. Kumaratunga ta rushe majalisar dokoki ta kuma girka sojoji a babban birnin kasar, a bayan da ta kori wasu manyan ministoci guda uku dake da hannu a shawarwarin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Wannan matakin ya zo a bayan da abokin adawar siyasarta, firayim minista Wickremesinghe, yake ziyara a nan Washington domin tattaunawa da shugaba Bush.

Mr. Wickremesinghe ya ce matakan da shugaba Kumaratunga ta dauka suna iya jefa kasar Sri Lanka cikin fitina. Shugabar ta sha zargin firayim ministan da laifin yin sassaucin siyasa fiye da kima ga 'yan tawaye.

XS
SM
MD
LG