Shugaba Bush ya bayar da iznin biyan tsabar kudi dala miliyan biyu tukuici ga duk mutumin da ya kamo tsohon shugaban kasar Liberiya, Charles Taylor, wanda ke zaman gudun hijira a Nijeriya.
Wannan kudin tukuici yana kunshe cikin dokar kasafin kudi dala miliyan dubu 87 na gudanar da ayyukan sojan Amurka a Iraqi da Afghanistan.
A jiya alhamis shugaba Bush ya sanya hannu kan dokar kasafin.
Za a yi amfani da kudin tukuicin na Liberiya domin kamo abinda dokar kasafin ta bayyana a zaman "wani mutumin da kotun bin kadin laifuffukan yaki a Saliyo ta tuhuma."
Ba a bayyana sunan wannan mutumi a cikin dokar kasafin ba. Amma kuma majiyoyin gwamnati da na majalisar dokokin Amurka sun shaidawa Muryar Amurka cewa ana batun Charles Taylor ne.
A watan Yuni wannan kotu ta musamman ta MDD ta tuhumi tsohon shugaban na Liberiya a saboda goyon bayan da ake zargin ya bayar ga 'yan tawayen kasar Saliyo.