Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Da 'Yan Tawayen Burundi Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya - 2003-11-17


Gwamnatin Burundi da babbar kungiyar 'yan tawayen kabilar Hutu ta kasar sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a wani yunkuri na kawo karshen yakin basasar shekaru goma a kasar.

Shugabannin Afirka da suka halarci taron kolin zaman lafiyar da aka yi jiya lahadi a Dar-es-Salaam a Tanzaniya su ma sun rattaba hannu kan yarjejeniyar, wadda ta kunshi yarjejeniyar raba ikon mulki tare da kuma cikakken shirin tsagaita wuta a tsakanin gwamnati da kungiyar 'yan tawayen mai suna Rundunar Dakarun Kare Dimokuradiyya a Hausance.

A bayan bukin rattaba hannun, shugaba Domitien Ndayizeye ya ce yana da kwarin guiwa wannan yarjejeniya za ta yi aiki. Amma masu fashin baki sun yi kashedin cewa ba za a iya cimma zaman lafiya na zahiri a kasar Burundi ba, har sai daya kungiyar 'yan tawayen kabilar Hutun kasar ta shiga cikin shirin samar da zaman lafiya.

A cikin sanarwar hadin guiwa da suka bayar, shugabannin yankin sun bai wa daya kungiyar 'yan tawayen ta kabilar Hutu mai suna Rundunar Dakarun Kwatar 'Yancin Kasa a Hausance wa'adin watanni uku da ta kawo karshen hare-hare, ta rungumi wannan shirin samar da zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG