Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kai wani gagarumin farmaki a Najaf da kufa - 2004-08-12


An kai wani gagarumin farmaki a Najaf da kufa:

Dakarun Amurka da na Iraqi sun kaddamar da wani gagarumin farmaki a biranen Najaf da Kufa, domin murkushe wani boren da mayaka an sai kai masu biyayya ga malamin shi'ar nan mai tsatsauran ra'ayi, Moqtada al-sadr , suka yi. Wata sanarwa daga sojin kawancen da Amurka ke jagoranta ta ce mayakan sun auna makamai zuwa cikin chaji ofis din 'yansanda dake Najaf daga wurin ibada nan mafi tsalki a birnin na Imam Ali. Sanarwar ta ce mayakan sai kan su kara da sojojin Iraqi nan da can, a tsakiyar birnin. Kawo yanzu, rundunar sojin ta ce an kai wannan farmakin ne da niyar kawar da mayakan a Najaf da Kufa. Sojin kawance sun ce an kai farmakin a wuraren da basu hada da wajajen ibada masu tsalki na biranen guda biyu ba. Sun kuma kara da cewa, suna bin ka'idojin da gwamnatin wucen gadi ta praminista Iyad Allawi ta shinfida mu su. Wannan samamen ya biyo bayan mako guda ana ta gwabzawa a tsakanin sojin Amurka tare na Iraqi dasu kuma mayakan sa kan a wasu biranen kasar da dama. A lokacin an kashe ko kuma an jikita daruruwan mutane. Magoya bayan shugaban 'ya shi'ar a bagadaza da kewaye da kuma wasu daga kudancin birnin Basra sun yi zangazangar nuna adawa a ayukan soji a kasar. A Basra ma, magoya bayan sun yi barazanar bututun mai idan har sojin Amurka basu janye daga Najaf ba.

XS
SM
MD
LG