Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tushen tagwayen gine-gine('Ground Zero') na tara maziyarta - 2004-09-10


Shekaru uku bayan hara-haren ta'addanci na sha daya ga watan Satumba kan cibiyar ciniki ta duniya dake New York wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane dubu uku maziyarta daga kasashen duniya sun mayar da wurin da yanzu ake kira 'Ground Zero' wato tushen ginin wani abin tarihi na duniya.

Banda wani rami a kasa babu wani abu da za'a iya gani a wurin da mutum dubu biyu da dari bakwai da casa'in da biyu suka halaka a lokacin harin kan tagwayen ginin. Ana gina sabon wani ofishi an kuma bude sabuwar hanyar zirga -zirga. Amma har yanzu ba'a fara aikin gina dandalin tunawa da mamatanba da kuma dogon ginin 'yanci wanda zasu maye dogayen tagwayen gine -ginen guda biyu ba.

Har yanzu masu ziyara suna yin tururruwa zuwa wurin. Wasu sukan dauki hotuna wasu kuma sukan dauki hotunan bidiyo. Wasu kuma sukan karanta bayanai kan abubuwan da suka abku a lokacin harin sha daya ga watan Satumba.Wasu kuwa sukan tsaya suyi shiru suna kallo. Nancy Vila 'yar shekara ashirin da biyar ma'aikaciyar shagon sayar da kaya daga Amsterdam Holland kamar sauran maziyarta tayi sintiri a kusa da babbar katanga mai tsawon mita hudu wadda ke zagaye da wurin.

Tace tana kokarin tuna irin tasirin wannan harin wanda ya jawo faduwar gine-ginen. 'Muna hutu ne a New York kuma muna so mu gani saboda dama muna da labarin komai tun ranar farko. Mun gani a labarai amma idan ka ga hotunan a labarai ba zaka yarda cewa abin ya abku haka ba. 'Zaka so ka gani a zahiri,' tace.

Nancy Vila tace ta hada da tushen ginin 'Ground Zero' a yanzu a cikin wuraren da ya zama dole ta gani a New York tare da ginin Empire da alamar mutun -mutumin 'yanci da kuma babban wurin hutawa da shahararren wurin sayar da kaya na Macy's da Bloomingdales. Da tagwayen gine-gine ne amma yanzu sai dai 'Ground Zero'.Wannan bai canja ba. Har yanzu wurin kallo ne,' tace.

Da dama daga cikin mazauna New York basa yarda cewa wurin da da ya kasance tagwayen ginin ya zama wurin zuwan 'yan yawon bude ido. Amma jami'an hukumar yawan bude na birnin sun tabbatar da cewa ziyartar wurin ya zama abu akai-akai ga maziyartan birnin New York.

Christyne Nicholas wadda ke shugabantar hukumar kula da yawon bude ido ta birnin tace hakika mutane sukan so su ziyarci zuciyar wannnan bala'i.'Bama mamaki dangane da wannan abu kuma yakan sanyaya zuciya . Ba talla muke ba wannan bai dace ba. Babu a cikin masu aikin kewaya da baki da suke maganar 'Ground Zero'. To amma bama hana mutane zuwa dole ne su samu sanyaya zuciya,' tace.

Babu kididdigar yawan mutanen da suka ziyarci wurin to ammma akwai kiyasi daga hukumar kula da tasoshin jiragen ruwa wadda ta mallakin wurin cewa mutane miliyan biyar zuwa takwas ne suka ziyarci wurin. Shirley Jaffe itace mai kula da ci gaban tattalin arziki na Alliance for Downtown wani kamfani mai kula da harkokin kasuwanci. Tace ziyartar tsohon wurin tagwayen gine-ginen ya zama daya daga cikin wurin ziyarar maziyarta.

'Ground Zero' wato tushen tsohon gine-ginen ya zama wani wuri da maziyarta suka ba mahimmanci. Babu wanda zai zo New York daga cikin Amurka ko daga waje bai je wurinba.Zuwa wurin ya zama kamar dole. Akwai hikima a gina gidan tarihi da wurin tunawa da wadanda suka mutu a wurin kuma zai zama an samar da wurin da maziyarta ya kamata suje,' tace.

Sonia Sumant daga Poona take a can India tace taga ya kamata taga wannan wuri da idonta. Na zama na damu da abinda ya faru a wannan wuri ta yaya ya faru, yaya girman abinda ya faru yake, kuma menene ya faru a zahiri. Ina so in gano me ya faru kuma inga irin barnar da aka yi a wurin. 'Hakika abin ya wuce sanin hankali,; tace.

Christyne ta kamfanin NYC tace ta yarda cewa barnar tana da ban tsoro musamman sai kaje 'Ground Zero'. Yana da mahimmanci mutane su san irin yadda barnar take.Mutane sun dauka cewa cibiyar ciniki ta duniya karamin wuri ne a Manhattan.(Digo shida da hekta biyar)babbaan wuri ne. Kuma idan ka je wurin kaga yadda abin ya abku to ba zaka manta ba. Sai kaje wurin sannan zaka fahimci komai. Babbar matsalar itace kasa mantawa.

Watanni bayan harin matsawar maziyarta ta sanya hukumar birnin gina wuraren tsayuwa don kallo kuma aka raba miliyoyin katunan shiga na kyauta. Yanzu wuraren an rufe su kuma maziyarta za su iya zagawa cikin yawancin harabar wurin.

Ma'ikatan gine-gine tuni sun fara gyara wurin don fara gina sabon dogon ginin 'yanci mai tsawon mita dari biyar da arba'in da daya da kuma husumiya mai mita tamanin da hudu zata kuma hada da hawa sittin na ofisoshi, hawa goma na wurin da za'a bayar haya da kuma wurin sa ido da kuma wurin injinan samar da makamashi.

XS
SM
MD
LG