Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin-tsaron Pakistan sun kashe wani dan al-Qaida - 2004-09-27


Hukumomin tsaro a Pakistan sun ce sun kashe wani mutumin da ake zargin babban dan al-Qaida ne, kuma wanda ake jin yana da hannu cikin kokarin da aka yi, har sau biyu, na kashe shugaba Pervez Nusharraf. Mr. Musharraf kuwa abokin Amurka ne na kud-da-kut a yakin da take da ta’addanci.

Jami’an suka ce an kashe shi wannan mutumin mai suna Amjad Hussain Farooqi a wata musayar wuta da dakarun-tsaro a garin Nawabshah dake kudancin Pakistan din. Tun daga bisani dai an ce za’a bada ladan dalar Amurka $ 300,000 ga dukkan wanda ya kashe shi mutumin, wanda akai ammanar cewa shine babbar wasila tsakanin kungiyoyin kasar masu tsatsauran ra’ayi da kuma kungiyar ta’addanci ta al-Qa’ida.

Ministan cikin gida Ahmed Sherpao ya shaidawa Muryar Amurka cewar shi dai Mr. Farooqi yana cikin wadanda ake zargi cikin wasu kulle-kulle guda biyu na kokarin kash Shugaba Musharraf din da aka yi a watan Disemban bara. Ya ce dakarun tsaron Pakistan sun kai wata mamaya ne bayan da suka sami wani labarin dake cewa shi farooqi na labe a wata unguwa. Ya ce “An kashe shi ne a lokacin wata arangamar da a cikinta yayi kokarin fasa jami’an tsaro ta hanyar jefa musu gurneti-gurneti.

Shi dai dama mashahurin dan ta’adda ne wanda kuma kowa ya sanshi da hakan kuma yana cikin masu hannu kan ayyukan ta’addanci da dama. Haka kuma shine ummul-khaba’isin kokarin da a kai har sau biyu na hallaka shugaban kasar Pakistan.

Har ila yau, ministan ya ce dakarun tsaron na kuma tsare da wasu mutane uku abokan shi Mr. Farooqi kuma ana nan ana yi musu tambayoyi. Ya ce kashe mutumin babbar nasara ce game da yakin da gwamnatin Pakistan ke yi da al-Qa’ida. Yace, “Babban nasara ce, domin kuwa kuwa yana cikin masu taka muhimmiyar rawa a kungiyar al-Qa’ida. Shi dai mutumin mai shekaru 30 da haihuwa ana zarginsa da sace da kuma fille kan ba Amurken Dan-jaridar nan Daniel Pearl a birnin Karachi cikin shekarar 2002. Mahukutan Pakistan suka ce Mr. Farooqi abokin mutumin kasar Libyan nan ne Abu Faraj Farj na kuda-da-kut. Shi kuwa Mr. Faraj shine babban mai kula da al’amurran al-Qaida a yankin, kuma ana jin yana nan a boye cikin Pakistan.

Ita kasar Pakistan din da aka sani a matsayin muhimmiyar kawar Amurka cikin yaki da ta’ddancin da take jagoranta, a yanzu haka ta kama kusan mutane 600 da ake zargin ‘yan al-Qa’ida ne ta kuma mika aglabiyyarsu ga Amurkan.

XS
SM
MD
LG