Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

kungiyar lafiya ta duniya ta kaddamar da riga kafin shan inna a kasashen - 2004-10-08


Kungiyar lafiya ta duniya da Asusun yara na majalisar dinkin duniya da sauran hukumomin agaji na lafiya sun kaddamar da yekuwar riga kafin shan inna mafi girma a kasashen Afirka guda Ashirin da uku(23). Kungiyar lafiya ta duniya ta ce tana fatar wannan riga kafin na bai daya zai farfado da kokarin da ta keyi na kawar da cutar baki daya. Yekuwar kawar da cutar shan innar ta gamu da cikas a bara, bayan da wasu jihohi uku da musulmi suka fi yawa a arewacin Najeriya suka kaurace ma riga kafin akan zargin ta na hana mata haufuwa kuma an gurbace ta.

Shugaban yekuwar kawar da cutar na kungiyar lafiya ta duniya, David Heymann ya ce, a lokacin da jihohin suka jingine shirin riga kafin, duk kasashen Afirka in banda Najeriya da Nijar sun riga sun yi salama da cutar a kasashen su. Mr Heymann ya ce sai dai yanzu, akwai kasashe goma sha biyu da aka halba da wannan cutar mai nakasa yara. Ya ce, amma ya yi imanin cewa yanzu da aka kaddamar da wannan riga kafin a Nahiyar Afirka a lokaci daya, za'a samu maslaha.

Mr Heymann ya ci gaba da cewa" kenan a yau mu na kyakkyawar fatar Afirka ta na nuna ma sauran duniya zata samu nasara, ta kuma cimma sauran kasashen duniya da suka riga suka kawar da cutar a nahiyoyin su. A lokacin da aka kaddamar da yekuwar kawar da cutar shan inna a cikin 1988, kasashe dari da ashirin da biyar ne ke da cutar kuma akallan yara dubu daya suke zama guragu a kowace rana. Kididdigar hukumar lafiyar, ta nuna cewa akwai masu dauke da cutar su 786 a kasashe shidda a duniya. A cikin wannan adadin, nahiyar Afirka dake cikin sahara ita ce ke da kusan sama da kashi tamanin.

Kungiyar lafiyar ta duniya ta ce masu riga kafin su milyan daya ne zasu yi aikin a kasashen Afirkan guda ashirin da uku, inda zasu shiga kauyuka da gida- gida domin digawa yara 'yan kasa da shekaru biyar maganin. Wakilin asusun yara na majalisar dinkin duniya a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka,Rima salah ya ce za'a yi amfani da duk abun da yakamata domin ganin an kai ga yaran.

_________________________________________________________________

XS
SM
MD
LG