Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kerry ya kammala kamfen na neman shugabancin Amurka - 2004-11-02


An fara zabe a Amurka bayan da dan takarar Democrat John Kerry ya kammala kamfen dinsa a kokarinsa na kayar da shugaba Bush. Bincike kan zaben ya nuna cewa ‘yan takarar suna kan-kan abinda ya sanya zaben ya zama mai ban mamaki. Senata Kerry ya bayyana a Wisconsin ranar talata da sassafe, jihar da binciken jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa ‘yan takarar biyu suna kan-kan. Mataimakansa sun ce senatan ya kammala kamfen dinsa a jihar ne saboda tana daya daga cikin ‘yan kalilan da su ke kyale ake rijista a kuma jefa kuri’a a ranar zabe.

Senata Kerry yana kokarin gabatar da wani kamfe guda daya a inda zai nemi mutane da su zabi jam’iyyar Democrat. Kerry a Florida A wuraren kamfe na karshe senata Kerry ya gayawa magoya bayansa cewa makomar Amurka tana hannunsu.’Wannan wani lokaci ne na musamman lokacin da Amurkawa za su yanke shawara , su ajiye duk wani banbanci na siyasa su yi amfani da hankalinsu, su duba makomarsu. Wannan shine lokacin da ya kamata su tuhumci Bush kan mulkinsa na shekaru hudu.’

Bayan da ya bar Wisconsin, senata Kerry ya zai je garinsa na Boston, Massachussetts a inda zai jefa kuri’arsa da rana. Ana sa ran zai ci abincin dare a wajen tarihi na gidan Union Oyster wadda ta zama al’adar bayan zabe ga senata Kerry. Mataimakansa sun ce zai kasance yana amsa tambayoyi ne ga gidajen talabijin ta hanyar tauraron dan Adam a jihar da ‘yan takarar suke kunnen doki.

Dan takarar Democrat da mataimakinsa senata John Edwards za kuma su saurari sakamakon zaben a daren talata. Akwai liyafa da aka shirya a dandalin Copley na Boston wanda zai ba abinda senata Kerry ya kira alamun bikin samun babbar nasara.

XS
SM
MD
LG