Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban ‘yan Democrat a majalisar dattijai ya sha Kaye, 'yan Republican na ci gaba da rinjaye - 2004-11-03


Jam’iyyar shugaba Bush za ta ci gaba da tabbatar da rinjaye a a majalisun dokokin Amurka bayan zaben ranar talata. A wani abin mamaki shugaban ‘yan Democrat a majalisar dattijai, Tom Daschle na mazabar Dakota ya sha kaye daga hannun dan Republican. .Mista Daschle ya zama shugaban’yan wata jam’iyya a majalisar da ya fadi zabe a cikin shekaru hamsin da suka wuce.

A zazzafan zabe da aka yi dan Democrat din daga kudancin Dakota ya rasa kujerarsa ga wani tsohon dan majalisar tarayya na jam’iyyar Repulican, John Thune. Da safiyar ranar laraba ne Mista Thune ya godewa magoya bayansa a wata liyafar samun nasara . ‘’Ba tare da wani bata lokaci ba yanzu da duku-dukun safiya ne amma kowa yana cike da murna’’ ya ce. ’Yan Republican sun fadada matsayin rinjayensu na kujera hamsin da daya a majalisar dattijai. Sun samu nasarar kujerar senatocin Democrat masu barin aiki a Goergia da North Carolina da South Carolina.

Dan majalisar Louisiana David Vitte ana zaton zai zama dan Republican na farko da ya ci zaben majalisar dattijai tun bayan yakin basasar Amurka a wannan jihar. ‘Yan Republican sun ci gaba da rike kujerunsu da gajeriyar rata a Oklahoma da Kentucky inda ‘yan Democrat suka yi fatan samun nasara. Barack Obama ‘Yan Democrat sun samu nasara a Illinois a inda senata a jihar , Barack Obama dan wani mutumin kasar Kenya mai uwa ‘yar Amurka ya ci zaben don maye kujerar senata dan Republican Peter Fitzgerald. Mista Obama , wanda ya gabatar da jawabin bude babban taron Democrat a watan Yuli zai kasance shine Ba’amurke dan asalin afirka kawai a majalisar dattijan Amurka a lokacin da sabuwar majalisar za ta fara zama a watan Janairu.Yana cike da kuzari a lokacin da ya yiwa magoya baya jawabi a daren talata.

‘’An karramani, dubi yawan mutane na gode muku ‘yan Illinois’’, ya ce. A Colarado babban lauyan Democrat Ken Salazar ana zaton zai ci zaben ya maye Ben Nighthorse Campbell na Republican wanda zai yi ritaya. A gaba daya za’a yi zabe a guraben majalisar dattijai guda talatin da hudu. Tom Delay A majalisar wakilai, a inda ake da kujeru dari hudu da talatin da biyar jam’iyyar Republican ta sake samun kujeru. Shugaban masu rinjaye Tom Delay ya yi murnar samun nasarar jami’yyarsa cewa kuma za ta ci gaba da zama mai rinjaye.’’Amurkawa sun bayyana matsayinsu a wannan daren da alama kuma za su ci gaba da rike majalisar wakilai karo na shida. a jere’’, ya ce.

Amma ita ma Republican ta rasa wata kujera mai mahimmanci ta dan majalisar Illinois Phil Crane, dan Republican da ya fi dadewa a majalisar a inda ya rasa kujerarsa ga dan Democrat Melissa Bean. A bangaren Democrat, sun rasa kujerun tsofaffin ‘yan majalisarsu daga Texas, Martin Frost da Charles Stenholm .

XS
SM
MD
LG