Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush ya sake samu wa'adi na biyu - 2004-11-04


Shugaba Bush ya sake cin zabe na wani wa’adin shekaru hudu. Shugaban mai ci, dan jam’iyar Republican ya yi jawabin samun nasara jim kadan bayan abokin hamayar sa na jam’iyar Damokarat, John Kerry ya amsa ya sha kaye. Mr Bush yayi jawabin ne a wani gini da aka sa wa sunan Ronald Reagan, tsohon shugaba kasa na jam’iyar republican wanda shine na karshe da ya samu zabe har karo na biyu a jam’iyar su.

Lokacin da yake jawabin, shugaba Bush wanda agajiye yake, ya dubi taron jama’ar dake yi ma sa murna, sai ya ce ma magoya bayan sa din “Amurkawa sun yanke hukumci.” Yace masu jefa kuri’a sun fito fiye da yadda aka saba gani abun da ya ba mu nasarar da ta kafa tarihi. A jawabin na sa Shugaba Bush ya fito karara, ya fada cewa yayi imanin mutanen Amurka sun zabe san ne domin ya ci gaba da manufofin sa na harkokin waje da lamuran cikin gida.

Yace Amurka zata shiga wani yanayi mai cike da fatan alheri a gida da ma waje, har ma ya ambato kasashen Afghanistan da Iraqi. Ana ganin kalaman sa sun kawo karshen mumunar barakar da ta kunno kai a lokacin zaben. Shugaba Bush ya yi fatan samu nasara bada jinkiri ba, amma sai kuma aka shafe tsawon dare guda a jihar nan mai mahimmanci ta Ohio ana ta, kirga kuri’u abun da ya jawo jinkirin.

Bayan ya ga alamar shugaba Bush yana kan gaba a zaben da tazara mai yawa, sai sanata John Kerry ya buga wa Mr Bush talho inda ya amince ya fadi zaben,wannan kuma ya zo sa’oi goma sha biyu bayan an rufe kada kuri’a ne. Bayan dan lokaci kadan, sai John Kerry ya sheda ma magoya bayan sa, cewa ya yarda ya yi aiki da shugaba Bush ne domin dinke barakar da ta kunno kai a dalilin siyasa a kasar.

XS
SM
MD
LG