Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana zaben shugaban kasa a jamhuriyar Nijar - 2004-11-16


Masu zabe miliyan biyar a jamhuriyar Nijar suna zaben shugaba a zagayen farko. Shugaban Nijar, Mamadou Tandja yana takara tare da mutum biyar amma ya ce yana sa ran sake cin zaben tun a zagayen farko.

Babban abokin hamayyarsa Mahamadou Issoufou na NPDS ya soki shugaba Tandja a inda ya ce ta hanyar magudi ne kawai wani zai iya cin zaben a zagaye na farko. Mataimakin shugaban jam’iyyar kuwa, Bazoum Mohammed ya ce ya yi imani zagaye na biyun na hudu ga watan Disamba za a yi shi ne tsakanin shugaba Tandja da Mista Issoufou. Mohammed ya ce ‘’ kowa ya sani a Nijar cewa ba zai yiwu ba wata jam’iyya ta lashe zabe a zagaye na farko. Ba zai yiwu ba. Idan aka lura da sakamakon zaben da aka yi na karshe, jam’iyyar da ke mulki ta sami kashi talatin da biyu ne.

Saboda haka za a yi zagaye na biyu da alama tsakanin shugaba Tandja da dan takararmu’’Shugaba Tandja ya kayar da Mista Issoufou a zaben alif da dari tara da casa’in da tara kuma shine shugaba na farko da ya kammala wa’adinsa na farko na shekaru biyar ba tare da an yi masa juyin mulki ba a cikin shekaru goma da kafa tsarin mulkin dimukuradiyya mai jam’iyyu da dama.

Mohamed ya zargi gwamnatin da rashawa. ’’Wannan zabe yana da mahimmanci ga Nijar saboda idan jam’iyyarmu ta kafa gwamnati za ta sauya manufofi musamman na tattalin arziki. A wannan gwamnatin akwai rashawa, muna da tsarin dimukuradiyya irin na kowacce kasar yammacin turai.’’. Shugaba Tandja ya bada karfi kan kiwon lafiya da ilimi a yankunan karkara a lokacin wa’adinsa a ofis. Jamhuriyar Nijar tana cikin kasashe matalauta kuma na kasa a ma’aunin ci gaban dan Adam na majalisar dinkin duniya. Sauran ‘yan takarar sun hada da tsohon firaminista da kakakin majalisar dokoki da minista da wakilin gamayyar Afirka ta AU a Sudan.

XS
SM
MD
LG