Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Ukraine ta jefa kuri’ar rashin goyon bayan gwam - 2004-12-01


Majalisar dokokin Ukraine ta jefa kuri’ar Allah wadai da gwamnatin firaminista Viktor Yanukovych wanda ke cike da rikicin neman shugabancin kasa da shugaban ‘yan hamayya , Viktor Yushchenko. Matakin ya zo a lokacin da masu sasantawa daga kasashen waje suka koma Ukraine don sabuwar tattaunawa kan wannan rikicin zabe tare da bagarorin biyu. Kadan ya rage majalisar dokokin ta kada kuri’ar da ka iya kawar da gwamnatin Yanukovych. Wannan kuri’ar Allah wadai ta biyo bayan gabatarwar ‘yan hamayya bayan da majalisar ta ki daukan irin wannan mataki a ranar talata. Kuma ta zo a lokacin da masu sasantawa suka iso Kiev dan tattaunawa tare da ‘yan takarar biyu da kuma shugaban kasar na yanzu , Leonid Kuchma.

Jami’in diflomasiyyar tarayyar turai, Mista Javier Solana ya shiga shirin tare da shugabannin [Polanda da Lithuania a kokarin kawo karshen matsalar. Ana sa ran ita ma Rasha za ta shiga shirin duk da kalaman shugaban Rasha, Vladamir Putin kan cewa ana samun hura wutar rikicin daga kasahen waje. Rasha na goyon bayan firaminsta Viktor Yanukuvych wanda aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben a zagaye na biyu na ashirin da daya ga watan Nuwamba duk da shaidun tafka magudi. Aiwatar da wani sabon zabe na daya daga cikin hanyoyin fita daga wannan rikici a lokacin da kasashen duniya ke kara kira da a samu yin zanga-zanga ta lumana da kuma yin amfani da matakan sharia don kawo karshen rikicin. Kiran Mista Yushchenko, na a sake wani zaben ya samu goyon bayan kasashen yammacin turai amma shi shugaba Kuchma ya dage cewa har in za a sake yin zaben sai an hada da sauran ‘yan takara.

Kotun kolin kasar ta ci gaba da sauraron karar da ‘yan hamayya su ka daukaka zuwa gabanta. Har yanzu zanga-zangar da ake yi a kasar ta lumana ce amma akwai barazanar barkewar rikici sosai abinda ya jawo kiraye-kiraye daga shugabnnin duniya wanda suka hada da Bush na Amurka kan a kara hakuri . Mista Bush ya ce ya yi magana ta waya da shugaban Poland, Aleksander Kwasniewski dan goyon baya ga sabon kokarinsa na sasantawa.. Ana kuma samun kiran samun daidaitawa daga Rasha. Boris Nemtsov na daya daga cikin 'yan siyasa masu sassaucin ra’ayi, ya kuma nemi da a samu daidaitawa kuma ya ce koma wanene shugaba dole ya yi aiki da ‘yan bagaren dayan indai ba so su ke su raba kasar ba . A wani abu mai kara kwarin gwiwa , yankunan da da su ke bayan Yanukovych kuma ke barazanar ballewa yanzu sun fara sauya matsayinsu.

XS
SM
MD
LG