Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan majalisar dokokin Amurka sun amince da sabuwar dokar tsaro - 2004-12-08


Ana sa ran majalisar dattijan Amurka za ta dauki mataki a ranar laraba wajen kawo manya-manyan sauye-sauye kan hukumomin asiri da tsaro na kasar. 'Yan majalisar tarayyar kasar a ranar talata sun amince da dokar sauye-sauyen da goyon bayan mutum dari uku da talatin da shida a inda 'yan majalisa saba'in da biyar ba su goyi baya ba.

Dokar ta nemi da kirkiro babban darektan ayyukan asiri da kuma cibiyar yaki da ta'addanci ta kasa wadda za ta rinka tattara bayanan sirri kan ayyukan ta'addanci. Daftarin dokar ya amince da mafi yawan shawarwarin da hukumar da ta binciki harin goma sha daya ga watan Satumba na shekara ta dubu biyu da daya ta bayar. Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka ya ce, shugaba Bush ya yi farin ciki matuka da amincewa da dokar da 'yan majalisar tarayyar suka yi, ya kuma yi imani zai sanya Amurka cikin cikakken tsaro.

Shugabannin majalisar tarayyar a ranar talata sun ce sun samu daidato a kan wasu bambance-bambance a dokar wanda ya jawo bata lokaci wajen amincewa da ita.

XS
SM
MD
LG