Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An nemi da a kara yawan dakarun Tarayyar Afirka a Dafur - 2004-12-10


Babbar kungiyar neman ‘yancin dan Adam a Amurka ta Human Rights Watch ta nemi Tarayyar Afirka (AU) da ta kara yawan dakarunta a Darfur don kare farar hular yankin. Kungiyar ta Human Rights Watch ta aikawa shugaba Obasanjo na Najeriya da wasika wanda shine shugaban Tarayyar Afirka, tana jaddada bukatar a kara yawan dakarun kungiyar a yankin Darfur.

Sama da dakaru dari takwas na Tarayyar Afirka ke a Darfur a yanzu da amincewar Sudan da kuma majalisar dinkin duniya. Ana sa ran nan da tsakiyar watan Janairu yawan dakarun tarayyar zai kai dubu uku da dari biyar. Amma Georgeette Gagnon ta Human Rights Watch ta ce wannan adadi bai isa ba musamman idan mutane miliyan daya da dubu dari takwas da yakin ya sa suka bar gidajensu suna son komawa gidajensu.

‘’Muna zaton cewa suna bukatar dakaru sama da dubu uku da dari biyar don yin aikin wanda ke bukatar tabbatar da tsaro a yankunan karkarar Darfur. Darfur na da girman gaske. Ya kamata a ce dakarun sun bazu zuwa yankunan karkara domin mutanen da yakin ya kora daga gidajensu da kuma wanda ke sansanonin ‘yan gudun hijira su samu tsaron da ya dace har su koma gidajensu da kansu. Amma wannan ba zai yiwu ba da dakaru dabu uku da dari biyar,’’ ta kara da cewa.

Kungiyar da ke da hedikwatarta a New York ta kuma ba da shawarar cewa, Tarayyar Afirka ta nemi kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da da ya bata cikakkiyar dama harkar. ‘’ Muna ga cewa akwai aiki a gaban kasa da kasa a kan Darfur, musammanma kwamitin sulhu wanda ya amince da wasu daftarori wadanda ba su da tasiri a zahiri. Wannan ya sa ana samun ci gaba da kai hare-hare kan farar hula daga bangaren ‘yan Janjaweed da dakarun gwamnati. Haka kuma ana samun keta yarjejeniyoyin daina bude wuta daga bangarorin ‘yan tawaye da dakarun gwamnati da ‘yan sa kai. Saboda haka babu wani ingantuwar yanayin da farar hula ke ciki,’’ ta ce.

Kungiyar Human Rights Watch ta kuma nemi da a yi maganar kiyaye ‘yancin dan Adam a duk tattaunawa kan samar da zaman lafiya ta kuma nemi da a dakatar da ’yancin Sudan na jefa kuri’a har sai yanayi ya inganta a Darfur.

XS
SM
MD
LG