Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

kasashen duniya za su agazawa wadanda suka gamu da girgizar kasa - 2004-12-27


Gwamnatocin kasashen duniya da kungiyoyin agaji na yin alkawuran taimakawa wadanda suka gamu da bala’in girgizar kasa wadda ta abkar da igiyar ruwa mai karfin gaske ta tsunamis wadda ta shafi mutane sama da miliyan daya a yankin gabar ruwa ta Bengal da yankunan bakin ruwa na kogin India. Wasu daga cikin ma’aikatan agajin da kayayyakin taimako tuni suna kan hanyarsu zuwa yankunan. Kasar Japan na cikin kasashen farko da suka yi alkawarin ba da taimako.

A ranar litinin gwamnati ta tura kungiyar ma’aikatan agaji mai likitoci ashirin da daya da ma’aikatan jiyya zuwa kasar Sri lanka. Shugaban tawagar shine Hiroyuki Yokota, wanda farfesa ne a sashen kula da aikin gaggawa a makarantar koyon aikin likita ta Nippon. Dokta Yokota ya ce tawagar na kokarin duba wadanda suka samu raunuka don haka suke kokarin isa wurin cikin sauri.

Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta Japan ta ce za ta bayar da kusan dala miliyan daya ga wuraren da igiyar ruwa mai karfi. Kuma tuni tana da wani sashe na agajin gaggawa wanda ke jira don taimakawa wajen samar da asibitin wucin gadi da kuma bayar da taimakon harkar lafiya. A Geneva, kungiyar agaji ta Red Cross ta duniya da kuma ta Red Crescent Societies na kiran da a samar da taimakon dala miliyan shida don taimakon gaggawa cikin hanzari don agazawa mutane kusan dubu dari biyar wadanda suka tsira da rayukansu masu bukatar taimako.

Firaminista, Manmohan Singh na India wadda shi ma kasarsa ke fama da matsalar igiyar ruwa mai karfin gaske ta tsunami ya ce ya rubutawa shugabannin Indonesia da Sri Lanka da Thailanda da na Maldives wasika yana sanar da su shirin taimakon kasarsa. Ministan harkokin kasashen wajen Australia, ya gayawa hukamar yada labaran kasarsa cewa kasarsa za ta bayar da taimakon gaggawa na kimanin dala miliyan bakwai . ‘’ Gwamnati za ta taimaka wajen bayar da taimakon gaggawa. Kuma za mu bayar da abinda ya fi haka nan gaba. Kuma za mu bayar da ruwan sha na kwalba da tantuna da sauran abubuwan da suka dace don taimakawa mutane,’’ ya ce.

Hukumar kasashen turai ta ce tana tuntubar ma’aikatanta a yankin da kuma sauran kungiyoyin bayar da agaji kamar su Red Cross don gano irin taimakon da aka fi bukata. Hukumar, ta kasashe ashirin da biyar ta yi alkawarin taimakon kudi har dala miliyan uku a matsayin taimakon farko. Dubannin mutanen turai da ‘yan Australia da ‘yan kasar Japan su ke hutu a yankin bakin ruwan Thailand da Sri Lanka da sauran kasashe a lokacin da igiyar ruwa ta jawo ambaliyar koguna a ranar lahadi.

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka ta White House ya ce Amurka za ta bayar da taimakon da ya dace kuma tuni ma wasu kayan agajin na kan hanyarsu ta zuwa Sri Lanka da Maldives. Jami’in ya ce Amurka za ta bayar da Karin taimako tare da wasu kasashen da wasu kungiyoyin duniya wanda suka hada da majalisar dinkin duniya. Kungiyar agaji ta Doctors Without Borders za ta aika da tan talatin da biyu na kayayyakin asibiti da na tsabta ta jirgin sama zuwa tsibirin Sumatra na Indonesia wurin da ke kusa da inda aka samu girgizar kasar.

XS
SM
MD
LG