Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana tsoron barkewar cututtuka sakamakon bala'in tsunamis - 2004-12-28


A lokacin da ake samun karuwar adadin wadanda suka mutu a sakamakon igiyar ruwa mai karfin gaske ta tsunamis ta ranar lahadi hukumomin lafiya na kokarin hana barkewar cututtuka a wuraren da ta fi shafa. Shi dai wannan bala’i ya shafi kasashe matalauta ne wadanda tsarin lafiyarsu ba zai iya kula da yanayin bala’in ba wanda ya jawo mutuwar kimanin mutane dubu arba’in. Hukumomi a kasashe goma na yankin tekun India wanda bala’in ya shafa na kokarin kawar da dubannin gawawwaki bayan da aka samu kazamar ambaliyar ruwa a yankunan bakin teku a ranar lahadi.

Masana kan harkar lafiya sun ce gawawwakin matattu da suka fara lalacewa ka iya gurbata ruwan sha. Dubannin mutanen da suka rasa matsugunai na cunkushe ne a sansanonin da aka samar marasa tsabta kuma ka iya haifar da cututtuka daban-daban. ‘’Hanyoyin samun ruwa sun gurbata,haka kuma harkar abinci ma matsala ce tun da mutane ba za su iya dafa abincinsu kamar yadda ya kamata ba. Za a samu matsalar wanke hannaye wanda zai iya sanadiyar barkewar gudawa kuma saboda irin yanayin danshi da gajiya da ake fama da su ka iya haifar da cutar da ta shafi numfashi,’’ in ji Dokta Han Heijnan mai kula da harkar tsabtace ruwa na hukumar lafiya ta duniya (WHO) a New Delhi.

Dokta Heijnan ya kuma ce dole ne a yi gaggawa don kare barkewar cututtukan. Girgizar kasa mai karfin 9.0 a yankin gabar ruwan tsibirin Indonesia na Sumatra a ranar lahadi ta haifar da igiyar ruwa mai karfin gaske a India da Sri Lanka da Thailand da Malaysia da Burma da Maldives da sauran tsibiran tekun India da kuma yankunan gabashin Afirka. Dubannin jama’a sun mutu wasu kuma sun bace.

A yankin tsibirin Maldives hukumomin lafiya na kokarin samar da dan taimako da za su iya bayarwa ga dubannin mutanen da suka tagayyara wasu ma a cikin lokunan tsibirin. Mataimakin darektan lafiya a Maldives, Dokta Moosa ya ce kasarsa ba ta da isassun likitoci da kuma kayan aikin da za ta iya magance manyan cututtuka. Ya kuma ce wadanda bala’in ya shafa na tare a wuraren da aka tanada kuma tuni har an fara samun barkewar cututtuka. Ya kuma kara da cewa akwai yanayin kazanta da matsalar rashin ruwan sha mai kyau.

Wasu masana kuma na nuna damuwa kan irin cututtukan da ba a gani da za su shafi wadanda bala’in ya shafa. Gloria Chen wadda ke magana da yawun kungiyar agaji ta Doctors Without Borders a Hong Kong ta ce matsalar cutar damuwa tana da wahalar warkarwa.’’ Daga irin abinda muka gani a baya, wadanda suka samu kansu a cikin irin wannan bala’i sukan samu damuwa mai tsanani da yake sun rasa wasu nasu kuma damuwar kan dade tare da su har watanni ko ma shekaru,’’ ta kara da cewa. Majalisar dinkin duniya ta ce wannan bala’i shine irinsa mafi muni a ‘yan shekarunnan kuma ta na kokarin shirya bayar da babban agaji.

XS
SM
MD
LG