Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kayan agaji na isa yankin tekun India - 2004-12-29


Wani babban shirin agazawa wadanda bala’in girgizar kasa da igiyar ruwa mai karfi ta tsunamis ya shafa a yankunan tekun India ya fara yin tasiri. Majalisar dinkin duniya dai ta yi kashedin cewa idan har kayan agaji bai fara isa ga wadanda bala’in ya shafa ba to ana iya samun barkewar cututtuka wadda ka iya jawo ninkawar mace-macen. An dai tabbatar da mutuwar mutane dubu saba’in a kasashe goma sha daya kuma wasu dubannin sun bace.

A can yankunan tekun India kayayyakin agaji kamar su abinci da ruwan sha da magunguna da kayan tace ruwa masu yawa duk sun fara isa. Amma majalisar dinkin duniya na kashedin cewa ba wai an gama aikin taimakon gaggawa ba ne. Dokta Nabarro na hukumar lafiya ta duniya ya ce akwai hadari muddin ba a raba kayan agajin cikin sauri ba don kare barkewar cututtuka. Ya kuma ce, ‘’ Ana iya samun mutane da dama su mutu sakamakon cututtuka masu yaduwa kamar yadda aka samu daga tsunamin.’’

Kungiyoyin agaji na duniya na kara kokarin bayar da taimako. Kasar Amurka ta yi alkawarin bayar da taimakon dala miliyan talatin da biyar kuma za ta aika da jiragen saman daukar kaya guda biyu don aikin agaji a yankin. Tarayya turai da kasar Japan da kuma Australia duk sun bayar da babbar gudunmawa. Wasu daga cikin wadanda suka tsira daga bala’in har yanzu ba a gano su ba. A Indonesia kungiyoyin ceto har yanzu na kokarin kai kayan agaji cikin lungunan tsibirin Sumatra wurin da bai wuce kilomita dari ba daga inda girgizar kasar karkashin tekun ta abku. Sojojin ruwan Indonesia sun isa garin Meulaboh wurin da gwamnati ta ce kusan rabin mutane dubu casa’in da biyar na mazauna gun sun halaka. A sauran wurare a gabar tekun ana iya samun mutanen da suka tsira amma ba su da ruwan sha da abinci da kuma wurin kwana. A gaba daya yankin, adadin wadanda suka mutu sai karuwa ya ke kuma wani karin abin damuwa shine irin yawan wadanda ba a gano ba . Wasu dai ba za a gano su ba. Wani shirin agaji babba na majalisar dinkin duniya wanda majalisar ta ce ba a taba ganin irinsa ba na kan hanya amma zai dauki lokaci kafin ya isa. A yanzu dai aikin agajin ana samunsa ne daga mutanen da bala’in ya shafa da kansu a kasashe goma sha daya da kuma daga bangaren gwamnatocinsu da ke a takure. Gwamnatin India tuni ta tura sojojinta don su kafa sansanononi inda su ke yin alluran rigakafin cutar kwalara da zazzabin typhoid da na cutar hanta. Sakataren jam’iyya mai mulki ta Congress, Ramesh Chennithala ya ce ana bukatar karin taimako.

Ita ma Sri Lanka ta tura sojojinta da kuma kungiyoyin sa kai don yin aikin agaji. A duk fadin yankin akwai dagewar mutanen gari wurin bayar da taimakon ruwan sha da abinci da mahalli da kuma taimakon kudi ga miliyoyin wadanda bala’in ya shafa sakamakon wannan girgizar kasa da igiyar ruwa mai karfin gaske ta tsunamis. Ana bukatar ci gaba da bayar da taimako na wani tsawon lokaci, wanda zai iya zama na shekaru kafin komai ya koma yadda ya ke a yankin.

XS
SM
MD
LG