Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firaministan Ukraine na kalubalantar sakamakon zabe - 2004-12-31


Firaministan Ukraine, Victor Yanukovych wanda aka soke zaben da ya lashe a baya a yanzu na kalubalantar sakamkon zaben zagaye na biyu na karshen mako. Wannan kalubalanta zai sanya daga lokacin fitar da sakamkon zaben abinda zai kara cecekuce kan zaben kasar. Hukumar zaben kasar ta tabbatar da cewa firaminista Yanukovych ya daukaka kara kan cikakken sakamkon wucin gadi na duk yankuna yana zargin yin babban magudi.

Kafofin watsa labaran yankin sun nuna hotunan Yanukovych tare da na hannun damansa suna shigar da kara a babbar hukumar zaben kasar wadda ke da kwana biyu ta duba korafinsa. Idan ta yi watsi da korafin kamar yadda dubannin 'yan kallon zaben kasashen waje suka yi to sai dai ya daukaka kara zuwa babbar kotun kolin kasar.

Shi dai Mista Yanukovych ya ki ya amince da sakamakon zaben ya kuma sha alwashin daukar duk wani matakin sharia kamar yadda abokin hamayyarsa, Mista Yushchenko ya dauka a baya bayan da aka ce an tafka magudin zabe a lokacin. Amma masu sharhi da dama suna ganin cewa Mista Yanukovych ba zai iya yin tasirin kirki ba ganin irin ratar da abokin hamayyarsa ya ba shi. Sakamakon dai ya ba wa Mista Yushchenko mai ra'ayin kawo sauyi maki goma sha daya kan shi Mista Yakunovych wanda ke da ra'ayin dangantaka da Rasha.

Mista Yushchenko ya nemi dubannin magoya bayansa da su taru a babban dandalin 'yanci na birnin Kiev a ranar talata. Mista Yushchenko ya ce kiran taron ministoci na ranar laraba ba ya bisa ka'ida ya kuma nemi magoya bayansa da su koma hana shiga ofisoshin gwamnati. 'Yan hamayyar sun amsa kiran sai dai ba kamar a baya ba sun kyale ma'aikatan gwamnati suna shiga ofisoshinsu a ranar laraba . Bayan wasu awanni kuma mai magana a madadin Yanukovych ya bayar da sanarwar janye taron ministocin. Su kuwa daruruwan mutanen da suke zaune a tsakiyar birnin Kiev tun sama da wata daya za su fara kwashe kayansu saboda bikin shigowar sabuwar shekara amma sun yi barazanar dawowa muddin sakamakon ya zama bai nuna nasarar Mista Yushchenko ba. A tsohuwar al'adar kasar shugaban kasa kan yi jawabi kan bukukuwan sabuwar shekara. To amma babbar tambaya a wajen 'yan Ukraine ita ce shin wanene zai yi musu jawabin , shugaba mai barin gado Kuchma ko wanda ake ga ya yi nasara a zaben da ya wuce, Mista Yushchenko.

XS
SM
MD
LG