Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Indonesiya na fatan  ‘yan tawaye za su ajiye makamai - 2005-01-10


Wani jami’in gwamnatin Indonesiya ya ce suna fatan ‘yan tawaye masu neman ballewa na yankin Aceh za su ajiye makamansu don shiga shirin sake gina yankin da igiyar ruwan tsunami ta yi wa barna. Alwi Shihab wanda shine ministan jin dadin jama’a na Indonesiya a ranar litinin ya ce duk da cewa an samu gabzawa tsakanin ‘yan tawayen da dakarun gwamnati tun bayan abkuwar bala’in tsunami na ranar ashirin da shida ga watan Disamba akwai fatan samun zaman lafiya.

Mista Shihab ya ce shugabannin addini da wasu shugabanni masu zaman kansu na tattaunawa da ‘yan tawayen wadanda ake kira GAM masu yakin neman cin gashin kai daga gundumar tun alif da dari tara da saba’in da shida. Ita dai GAM ta yi shelar dakatar da bude wuta bayan abkuwar girgizar kasa da igiyar ruwan tsunami.

‘’Akwai tattaunawa ta bayan gida . Akwai kuma tuntubar da shugabannin addini su ke wa GAM don shawo kansu kan cewa wannan dama ce ta samun zaman lafiya a Aceh. Dukkanin duniya na tare da Aceh kuma wannan lokaci ne na ajiye makamai’’, in ji Mista Shihab. Yankin Aceh, yana arewacin tsibirin Sumatra wurin da ya gamu da barna mai tsanani sakamakon igiyar ruwan tsunami. Sama da mutane dubu dari da hamsin ne suka halaka a yankin a kasashe goma sha biyu na yankin tekun Indiya a inda kashi biyu cikin ukunsu a yankin Aceh su ke. Daruruwan ma’aikatan agaji ‘yan kasashen waje na yankin Aceh a wani shirin agaji na kasa-da-kasa da babu irinsa a tarihi. Amma sai dai akwai fargba kan lafiyarsu saboda rikicin ‘yan tawayen masu neman ballewa daga kasar.

Mista Shihab ya ce shugaban kasar Susilo Bambang Yudhoyno na fatan cewa bangarorin biyu za su dakatar da fada a kuma bayar da karfi wajen taimakawa dubannin mutanen da bala’in tsunami ya shafa. ‘’Ina ga cewa ya kamata bangarorin biyu su lura da kiran shugaban su kuma yi la’akari da makomar Aceh da kuma ci gabanta, ‘’ ya kara da cewa. A lokacin da aikin agaji ke kankama wani jirgin sama mai sauka r ungulu na sojan ruwan Amurka ya yi saukar gaggawa a ranar litinin a wani filin shinkafa a kusa da filin jirgin saman Banda Aceh yana kuma dauke da ma’aikatan jirgin guda goma. Da damansu sun samu kananan raunuka.

Rundunar sojan ruwan Amurka ta dakatar da tashi da saukar jiragen samansu zuwa wasu ‘yan awanni ana kuma gudanar da bincike. An kuma samu wata motsawar kasa da sanyin safiyar litinin wadda ta kai ma’auni shida da digo biyu abinda ya jawo fargabar jama’a da kuma guje-guje a kan tituna.

XS
SM
MD
LG