Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar dinkin duniya ta shirya babban taro kan bala' oi a Japan - 2005-01-18


Makwanni uku bayan girgizar kasa da igiyar ruwa mai karfi ta tsunami suka yi barna a yankin tekun Indiya daruruwan kwararru da jami'an gwamnatoci na taro a Japan cikin wannan makon domin gano yadda za a rage irin asarar da ake yi sakamakon irin wannan bala'oi. Za su yi wannan taron ne a birnin Kobe birnin da shi kansa ya yi fama da bala'in girgizar kasa mai karfin gaske shekaru goma da suka wuce.

Majalisar dinkin duniya na jagorancin wani babban shirin agaji a yankin tekun Indiya don taimakawa miliyoyin wadanda suka gamu da bala'in girgizar kasa da igiyar ruwa ta tsunami ta ranar ashirin da shida ga watan Disamban bara. A wani bikin maraba da masu halartar taron a wani otel a ranar talata, sarkin Japan Akhito ya yi wa mahalartan sama da dubu hudu maraba. Sarkin ya kuma ce yana fatan irin halin da Japan ta samu kanta a ciki a baya da kuma fasahar ta kan rage illar bala'oi zai taimakawa sauran bangarorin duniya wajen rage masifar da ke tattare da bala'oi.

Birnin Kobe na daya daga ckin alamu a fili na irin yadda za a iya sake gina birnin da ya hadu da wani bala'i. Daya cikin hudun birnin Kobe ya lalace a lokacin bala'in girgizar kasar shekaru goma da suka wuce amma yanzu an sake gina kusan dukkanin birnin. Babban magatakardar majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya gayawa wakilai masu halartar taron ta kaset din bidiyo cewa dole ne a kashe kudi waje shirin kare kasashe daga bala'oi da kuma rage asarar rayuka sakamakon wadannan bala'oi. Daya daga cikin abubuwan da za a bawa mahimmanci a lokacin wannan babban taro shine yadda za a samar da na'urar gano igiyar ruwan tsunami wadda za ta iya kula da duk fadin duniya. Japan dai na da irin wannan na'ura ita ma Amurka na da ita wadda ke lura da duk fadin yankin tekun Pacific amma babu a yankin tekun Indiya.

Masana da dama sun ce na'urorin bincike na seismic da marine bouys ka iya gano manyan igiyoyin ruwa irin wanda suka yi barna a yankin a watan da ya wuce kuma ka iya ba gwamnatoci lokacin da za su gargadi mutanensu don su gudu zuwa wurare masu tudu. Bayan lokacin tattaunawa na kwararru kan abubuwa da dama kamar yadda za a inganta lafiyar wadanda suka gamu da bala'oi mahalartan ana sa ran za su fitar da kuduri kan yadda za a rage irin barnar da ke abkuwa sakamkon bala'oi a duk fadin duniya.

A ranar talata Japan ta bayar da sanarwar wani shirin rage bala'oi ta hanyar amfani da shirinta na taimakawa kasashen waje. Kodayake babu adadin kudin na wannan shirin firaminista Junichiro Koizumi ya ce kasarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen musayar bayanai da kuma bayar da taimako wajen gano mutane ta hanyar kudi da kuma na'urori

XS
SM
MD
LG