Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon shugaban jam’iyyar gurguzu ta Sin, Zhao Ziyang ya rasu - 2005-01-18


Tsohon shugaban jam’iyyar gurguzu ta Sin Zhao Ziyang ya rasu a ranar litinin a wani asibitin Beijing yana da shekaru tamanin da biyar bayan da ya shafe shekaru goma sha biyar karkashin daurin talala. Ana tuna Zhao Ziyang a matsayin daya daga cikin wadanda suka kawo sauyi a tsarin tattalin arzikin kasar mai bin tafarkin gurguzu wada ya fadada kasuwanci da sauran kasashen duniya.

Kokarinsa na kawo sauye-sauyen siyasa a Sin ya jawo masa samun magoya baya masu yawa amma kuma ya hadu da fushin masu tsattsauran ra’ayin gurguzu a lokacin da ya ke sakataren jam’iyyar a farkon shekarun alif da dari tara da tamanin.

Joseph Cheng wanda farfesa ne na kimiyyar siyasa a jami’ar birnin Hong Kong ya ce Ziyang ya zama wani tauraron goyon bayan kawo sauye-sauyen siyasa a Sin a inda ya goyi bayan dalibai masu zanga-zanga a dandalin Tiananmen. Zhao Ziyang ya shafe shekaru goma sha biyar karkashin daurin talala saboda goyon bayan da ya nuna ga dalibai masu zanga-zanga a alif da dari tara da tamanin da tara a inda aka kashe daruruwa ko ma dubanni mafi yawanci matasa. Shugabannin a lokacin sun sauke Mista Ziyang suna zarginsa da kokarin raba kan jama’iyya kuma tun daga lokacin ba a sake jin duriyarsa ba.

Sanarwar gwamnati kan mutuwarsa an takaita ta a inda kamfanin dillancin labaran gwamnati ya sanar da cewa ya yi fama da ciwon zuciya da na huhu na wani lokaci. An dai kara yawan jami’an tsaro a dandalin Tiananmen saboda jita-jitan cewa za a iya samun barkewar zanga-zanga. Amma mutane kadanne suke ganin cewa za a iya yin zanga-zangar.

Ita dai gwamnatin Sin ta hana yin duk wata tattaunawa ko wani taro kan tunawa da murkushe zanga-zangar ta Tiananmen. A duk ranar hudu ga watan Yuni ‘yan sanda sukan kama duk wasu masu kira ga gwamnati da ta sauya bayaninta kan wannan abu da ya faru. Masu neman sauyi na kiran da gwamnati kan ta sauya dokarta kan zanga-zangar alif da dari tara da tamanin da tara wanda jami’anta suka kira wani zagon kasa ga juyin-juya-hali. Awanni bayan sanarwar mutuwar Ziyang irin wannan kiraye-kiraye na kawo sauyi sun sake tasowa.

Wani tsohon mai fafutukar samar da mulkin dimukuradiyya Ren Wanding ya tuna irin rokon da Zhao Ziyang ya yi cikin kwalla a watan Mayu na alif da dari tara da tamanin da tara a lokacin da ya je dandalin Tiananmen ya roki dalibai da su koma gidajensu don gudun kada sojoji su murkushe su. Bayan da aka samu labarin mutuwar Mista Zhao a ranar litinin Mista Ren ya bayyana marigayin a matsayin wani ginshikin samar da dimukuradiyya ya kuma yi fatan gwamnati wata rana za ta sake bincikar hadarin na alif da dari tara da tamanin da tara. Amma ya ce baya tsammanin wannnan abu a nan kusa.

Ya ce, ‘’ jam’iyyar gurguzu ta Sin ba ta taba yadda cewa yin amfani da karfin soja kan masu zanga-zanga a alif da dari tara da tamanin da tara kuskure ne ba. Babban burin jam’iyyar shine su kare mulkinsu. Ba sa goyon bayan duk wata kungiya mai goyon bayan dimukuradiyya.’’ Masu nazari kan al’amura sun ce da alama gwamanati ba za ta ba mutuwar Ziyang wani mahimmanci ba don kada a samu wani cece-kuce. Sun kuma ce shugabannin na tsoron cewa mutuwarsa ka iya zama wata dama ta hada kan manoma matalauta da marasa akikin yi da sauran masu ra’ayin kawo sauye-sauye a Sin.

XS
SM
MD
LG