Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush na Slovakia don tattaunawa da Putin - 2005-02-24


Shugaba Bush na Amurka na Slovakia don tattaunawa da shugaban Rasha Vladamir Putin . Wannan ziyara ita ce ta karshe a jerin ziyarsa a Turai. Shugaba Bush na fuskantar babban kalubale a Bratislava na karfafa dangantaka da shugaban Rasha a lokacin da zai nemi ya kara mutunta ‘yancin jama’a.

Akwai damuwa cewa Rasha ba za ta cika alakwarinta na mutunta ‘yancin dan Adam ba. A lokacin da shugaba Bush ke magana da ‘yan jaridu ranar Talata a Brussels ya ce yana fatan ganin tattaunawarsu da shugaban Rashan. Ya kuma ce, ‘Akwai kyakkyawar dangantaka tsakanina da shugaba Putin kuma tana da mahimmanci domin tana sa ni da kasa ta mu tunawa Putin cewa dimukuradiyya na kafuwa ne bisa doka da kuma girmama ‘yancin dan Adam da mutunta shi da kuma ‘yancin ‘yan jaridu.’’

An dai tattauna halin da Rasha ke ciki a lokacin ganawar da shugaba Bush ya yi da shugabannin Turai a Brussels hedikwatar kungiyar tsaron NATO da kuma Tarayyar Turai. Shugaba Bush ya ce kasashen yankin Baltic na daya daga cikin masu shakku kan niyyar Rasha. ‘’Ina fatan gabatar da sakonsu wanda ke da mahimmanci ga shugaba Putin domin ya yi bayani sosai kan wasu matakai da ya dauka ya kuma girmama makwabtansa,’’ ya ce. Mista Bush ya yi hasashen cewa tattaunawar ta su za ta yi armashi a inda ya jaddada cewa yana da mahimmanci a samu kyakkyawar dangantaka tsakanin Amurka da Rasha. ‘Muna da abubuwa da yawa da za mu iya yi tare muna da manyan ayyuka da za mu iya yi tare kamar tabbatar da tsaro a duniya ta hanyar tabbatar da hana yaduwar kayayyakin nikuliya.’’ Ya ce.

A dai dai lokacin da za a fara yin wannan taron tattaunawa na Bratislava mai bayar da shawara kan tsaron kasa a fadar gwamnatin Amurka Stephen Hadley ya ce duniya na sa ido don ganin ko Mista Vladamir Putin zai cika alkawarinsa na tabbatar da dimukuradiyya. Amma ya kuma jaddada cewa har yanzu samar da dimukuradiyya a Rasha wani batu ne da ke jkan hanya.Ya kuma ce Rasha za ta lura cewa a karni na ashirin da daya karfarfar Rasha ita ce Rashan da ke bin tafarkin dimukuradiyya.

XS
SM
MD
LG