Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu zanga-zanga a Beirut sun yi watsi da hanin hukuma - 2005-02-28


Awanni kafin majalisar dokokin kasar Lebanan ta jefa kuri’ar rashin amincewa da gwamanati dubannin jama'a dauke da tutoci sun yi zanga-zanga a dandalin shahada da ke Beirut. Yanayin na cike da ratsa jiki a inda dubannin masu zanga-zangar suka nemi janyewar dakarun Syria daga Lebanan da kuma saukar gwamnatin kasar. Zanga-zanga na karuwa tun bayan kisan gillar da aka yi wa shahararren tsohon firaministan kasar Hariri a farkon wannan watan jiya. Masu zanga-zangar sun yi imanin cewa akwai hannun Syria a kisan abinda ita Syria ta karyata. ‘Yan siyasa masu hamayya sun shiga cikin taron masu zanga-zangar a inda da dama daga cikinsu suka kwana a dandalin don gujewa dokar hana fitar dare da gwamnati ta kafa.

Wani tsohon dan majalisa kuma babban dan hamayya Butros Harb ya shaidawa masu zanga-zangar cewa ‘yan hammayar za su ci gaba da yin tawaye har sai ran da Lebanon ta kwato ‘yancinta. Sojan Lebanon sun toshe mafi yawancin hanyoyin shiga birnin Beirut don aiwatar da dokar hana fitar dare da aka sa, sai dai sun kyale masu zanga-zangar sun taru. A yau ne dai majalisar dokokin Lebanan za ta yi mahawara kan batun yin Allah wadai da gwamnatin firaminista Omar Karameh mai samun goyon bayan Syria.

Shi da firaminista Omar ya gayawa gidan talabijin na al-Arabiya cewa gwamnatinsa na ci gaba da samun goyon bayan mafi yawancin jama’ar Lebanon. Su dai ‘yan siyasa masu hamayya na kiran da a kafa gwmanatin hadin kan kasa ta rikon kwarya da kuma janyewar dakarun Syria kusan dubu goma sha hudu daga Lebanon. Syria ta ce a shirye ta ke da ta yi amfani da yarjejeniyar alif da dari tara da tamanin da tara wadda ta nemi da ta kai dakarunta zuwa kwarin Bekaa amma ta ce babu maganar janyewa gaba daya. Amurka da Faransa sun gayawa Syria cewa dole ne ta mutunta kudurin majaliasar dinkin duniya na 1559 wanda ya nemi da Syrian da ta janye dukkanin dakarunta daga ‘yar karamar makwabciyarta .

Dakarun Syria sun fara shiga Lebanon ne a shekarar alif da dari tara da saba’in da shida ‘yan watanni bayan barkewar yakin basasar kasar sun kuma kasance a kasar tun wancan lokacin suka kuma mamaye siyasar kasar.

XS
SM
MD
LG