Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an kiwon lafiyar kasar Angola  sun ce yawan wadanda su ka halaka sanadiyar matsananciyar cutar da ake kira Marburg Fever ... - 2005-04-12


Jami’an kiwon lafiyar kasar Angola sun ce yawan wadanda su ka halaka sanadiyar matsananciyar cutar da ake kira Marburg Fever ko Virus de Marburg, ya kai 203 daga cikin mutane 221n da aka san sun kamu da ita.

A jiya litinin jami’ai sun fada cewa al’amarin ya fi yin muni a yankin lardin Uige da ke arewacin kasar inda mutane 184 su ka rasa rayukan su saboda cutar wadda ta fara kulla a watan oktoban da ya gabata.

Yanzu haka, likitocin da ke jinyar marilan da ke fama da cutar ta Marburg Fever ko Virus de Marburg, na bada shawarar rufe wani babban asibiti a lardin Uige saboda a cewar su, akwai bukatar fesa maganin kashe kwayoyin cuta a babban asibitin.

Ƙungiyar agajin jin kai ta likitocin duniya da ake kira Doctors Without Borders ko Medecins Sans Frontieres, ta ce daukan wannan mataki ya zama wajibi domin a rage hadarin yaduwar cutar a babban asibitin inda masu fama da munmunar kwayar cutar mai kisa, ke zaman kakaita, an keke su.

Cutar mai haddasama dan Adam zubar jini daga cikin tumbi, da hanji da kuma sauran kayan ciki , mai kama da cutar Ebola ta yaɗu ne ta hanyar duk wani ruwan da ke fita daga jikin mutu, sannan kuma nan da nan ta ke kisa.

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ko OMS ta tura tawagogin jami’an ta zuwa kasar Angola domin kawar da gawarwaki da kuma gano waɗanda su ka yi cukanya da wadanda su ka kamu da cutar.

XS
SM
MD
LG