Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Praim ministan kasar Iraqi mai jiran gado ya kammala zana sunayen wadanda ya ke son ba ma mukamai - 2005-04-27


Praim ministan kasar Iraqi mai jiran gado ya kammala zana sunayen wadanda ya ke son ba ma mukamai a gwamnatin shi bayan an yi watannin ukku ana tafka shawarwarin siyasa.

A jiya talata Ibrahim al-Jaafari ya mika jerin sunayen ga shugaba Jalal Talabani. Majalisar shugabancin kasar Iraqi mai wakilai ukku, ta amince da sunayen , kafin su isa gaban majalisar dokokin kasar mai wakilai 275, domin ta yi kuri’ar amincewa da su.

Jami’an Iraqi da gidan telebijin kin gwamnati sun bada labarin cewa ’yan Shi’ar kasar masu rinjaye za su samu mukamai 17 a gwamnatin, su kuma Kurdawa da su ka zo na biyu a zabe, za su samu mukamai 8. ‘Yan ahlil Sunna , wadanda akasarin su, kauracema zaben su ka yi, za su tashi da mukamai 6. Sannan kuma Kiristocin kasar ’yan dalilan za su samu mukami daya tallin tal.

Ga dukan alamu, a sabuwar gwamnatin, ban da jam’iyyar praim ministan rikon kwarya Iyad Allawi wadda ta samu kujeru 40 a majalisar dokoki. Bugu da kari ma, Mr. Jaafari ya nada mataimakan Praim minista ukku: dan Shi’a daya, Bakurde daya, da kuma dan ahlil Sunna guda.

A halin da ake ciki kuma praim ministan kasar Italiya Silvio Berlusconi ya ce , har yanzu ba’a gama binciken da ake gudanarwa game da kisan da sojojin Amurka su ka yima wani jami’in leken asirin Italiya a watan jiya ba.

A jiya talata ya nuna bakin cikin shi game da abun da ya bayyana a zama rahotannin tsegumin ban takaicin da ke cewa binciken zai wanke sojojin Amurka daga laifin da aka dora mu su.

Sakataren tsaron Amurka Donald Rumsfeld ya ce har yanzu kasashen biyu ba su cimma jituwa akan wani rahoton hadin guiwa ba.

A shekaran-jiya litinin jami’an Amurka su ka ce rahoton zai daddale cewa galibi sojojin Amurka sun bi umarni kamar yadda ya kamata, lokacin da su ka bude wuta kan wata motar da ke dauke da jami’in leken asirin Italiyar da kuma wata ’yar jarida a birnin Baghadaza. Jami’an sun ce a guje motar ta nufi wani wurin duba matafiya, sannan kuma direban ta ya yi banza da umarnin rage wuta---Hukumomin Italiya sun ce jikin su, zar kunne, game da wannan bayani.

Harbin da sojojin Amurkar su ka yi ne, ya kashe jami’in leken asirin Italiya Nicola Calipari , ita kuma ’yar jarida Giuliana Sgrena, ta jikkata; idan ba ku manta ba ita ce ’yar jaridar kasar Italiyar da ’yan tawayen kasar Iraqi su ka saka bayan sun dade su na yin garkuwa da ita.

XS
SM
MD
LG