Shugaba Umar Hassan Al Bashir
na Sudan, ya kai ziyara kasar Masar, a wani abu da ake wa kallon bijirewa
sammacin da kotun kasa da kasa mai hukunta laifuffukan yaki ta ta bayar na a kamo
mata shi ne.
Shugaba Hosni Mubarak
shine ya taryi Mr. Bashir a filin Jirgin saman birnin Alkahira, daga nan kuma
suka zarce kai tsaye da tattaunawar da jami'an kasashen biyu suka ce ta karkata
ga wancan sammaci na kamo shugaban na Sudan.
Kotun ta kasa da kasa ta
bukaci kasashen duniya da su taimaka a kamo mata Shugaba Al Bashir, amma babu
alamun cewa Masar zata amsa wannan kira.
Ministan Harkokin Wajen
Masar, Ahmad Aboul Gheti, ya fada a jiya Laraba cewa Masar bata amince da yadda
kotun ke muzanta Al Bashir ba.
Masar dai tana daga cikin kasashen da basu sanya hannu a yarjejeniyar kafa kotun ba.